✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallar Layya: Hanyoyin kayatar da Maigida

Assalamu Alaikum; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili; da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga…

Assalamu Alaikum; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili; da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani ga Uwargida kan hanyoyin da za ta bi don kayatar da maigidanta ranar Sallah; Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya zan ya amfani dukkan ma’aurata kuma ya kara armashin so da kauna a tsakaninsu, amin.

1.    Ki burge shi da kyautar ban mamaki: Kyauta babbar hanya ce ta nuna so da kauna tsakanin mutane musamman masoyan juna; to me ya sa kodayaushe mata mu ne masu amsa, amma da wuya mu bayar? Duk dai namijin aka sani da bayarwa mace kuma da amsa, amma shi ma maigidan in aka yi masa kayatacciyar kyauta zai ji dadi don zai san lallai an damu da shi. Maigida kullum yana cikin dawainiya da ke, sayo wannan yau gobe wancan, amma yawancin  mata sai ka ga har shekara ta zo ta shige ba su ba mazansu wata kyauta ba in ban da ta al’ada: watau kyautatawa irin ta zaman aure. Ran sallah rana ce da kowa ke son ya ga ya kyautata ga mafi kusanta gareshi; don haka uwargida a daure a zabi babbar kyauta ta ban mamaki a yi wa maigida; sai ki zabar masa irin abinda kika san yana matukar so; abinda kike ganin zai sa ya ji dadi sosai kuma ya yi farin ciki, koda kuwa kudi ne ko wani abu daban, in dai zai kayatar da shi to shi za ki ba shi. Kuma ki kawata kyautar taki, in wacce za ta rufu cikin takarda mai walkiya ne sai ki sa, ki dan hada da ’yar takarda mai dauke da kalaman nuna so da kauna da godiya da jin dadin zama da shi, misali:
“Masoyina, abin kaunata; Ban san irin kalaman da za su isa ga nuna godiya ta gare ka ba: Kana matukar burge ni, ina jin dadin zama da kai fiye da komai; Ina tsananin godiya ga Allah madaukakin Sarki da Ya zaba min kai a matsayin mijina; Ba wani maigida da ya kai ka a duk duniyar nan; Ina matukar sonka fiye da yadda kake zato; ina alfahari da kuma ji da kai fiye da yadda uwa ke ji da dan autanta”.
Da sauran dai kalaman jin dadi makamantan wadannan; wannan zai kara sawa ki shiga ran shi sosai ki kwanta male-male cikin zuciyar sa; to balle kuma ace ki saba ma shi da abubuwa makamantan haka?
2.    Ki shirya masa daren Shagalin kauna: Ran daren sallah, sai Uwargida ta yi shirin ba maigidanta babbar kayatarwa a shimfidar aurensu; daman kin gyara dakin auren ku kin kawata shi, in da hali ki sami zanen gado na siliki ki shimfida; ki sanyaya dakin da turare mai  kamshi; ki kashe fitilun dakin ki kunna kyandir guda biyu don za su ba dakin sigar kaunatayya. Ke ma ki cakare da kayan barci masu laushi kuma masu shara-shara, fuskarki ta ji kwalliya sosai, ki feshe jikin ki da turare mai tsananin dumamawa da tsumamawa; Sai ki fara da gabatar da kayatacciya kuma lallausar tausa ga maigida, ki shimfida tawul-tawul bisa gadon inda za ki masa tausar, sai ki bi duk jikin ki na luguiguidawa  da man zaitun, ki fara da yatsu da tafin kafa, sai bayan wuya da baya gabadayan sa, don wadannan wurare ne su ka fi tara gajiya. Sannan sai saman kai; kugu da sauran jiki duka, kina yi kina rada ma shi kalaman so da kauna da motso da sha’awa; duk ki bi wata tsohuwa da sabuwar gajiyar da ke jikinsa ki matseta ki ga cewa kin fitar da ita; da farko za ki rika yi ki na dan sa karfi a yatsun ki, amma in kin fahimci jikin ya tausu sosai, to sai ki koma kina tausawa sama-sama kuma kadan-kadan.
Tausa (ta sosai din) ta na da matukar alfanu ga lafiyar jiki da  ma’aikatar hankali, don haka ma’aurata a rika yi ma juna haka ko da sau daya a wata ne. Wajen gabatarwar ibadar aure a ranar ki ba shi mamaki kuma ki burge shi sosai, duk abinda ya ke so ki yi masa, ki cire duk wani tsaiko ko wani shamaki, ki wuce iyakar ki, wannan dare, ki ba shi daren da zai dade yana tunawa; wanda zai sa ya ji ba fa namijin da ya kai shi tunda shi ya yi sa’ar samun ki.
Duk da dai ranar sallah ranar ciye-ciyen kayan makulashe da tande-tande ne, ya na da kyau in uwargida za ta shirya daren shagalin kauna ta wuni a ranar tana shan kayan marmari, ’ya’yan itace da  ganyayyaki, ta kuma sha ruwan kwakwa, kunun aya da markadadden karas da duk wani abu mai alfanu da ta san yana agaza mata ta wannan fannin.
3.    Jiyar da shi dadi ta cikin wasika: Zama za ki yi Uwargida, ki tsara  wasika zuwa ga maigidanki; wasikar tana iya kasancewa ta soyayya, ta godiya, ko ta yabo, ko ma ki hada duka ukkun cikin wasika daya. ki cika ta da kalamai masu dadi na so da kauna, ki yabe shi yabo na gaskiya, kuma ki gode masa isashshiyar godiya, musamman in kika duba irin dawainiyar da ya sha ta saye-sayen kayan sallah da kuma hidimomin abincin Sallah, ragon layya, da sauransu. Sannan in da hali ki yi amfani da fensir mai kala ki zana furanni masu kyau cikin wasikar, ki kawata su kuma ki dan sassaka wasu kalaman soyayya a ciki, kamar dai irin yadda ake wa saurayin da ake so a shekarun da rubutun wasika ke tashe. Sannan ki samu turare mai  kamshi ki dan fesa, sai ki sa a ambulan ki saka masa inda zai gani, misali cikin aljihun kayan Sallarsa, ko cikin battar sa ta saka kudi (wallet) ko ki aje masa a inda kika san ba mai gani sai shi.
Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.