✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah: Zulum Ya Biya Ma’aikatan Borno Albashin Afrilu

Zulum, ya amince da biyan albashin ma’aikatan jihar na watan Afrilu domin su samu damar gudanar da bikin Karamar Sallah cikin walwala.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da biyan albashin ma’aikatan jihar na watan Afrilu domin su samu damar gudanar da bikin Karamar Sallah cikin walwala.

A cewarsa, ma’aikatan jihar sama da 16,000 za su samu albashinsu na watan Afrilu, don su samar damar yin bikin karamar sallar da ke tafe a karshen mako cikin farin ciki.

Mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau ne, ya kara cewa Zulum ya yi kira ga daukacin al’ummar Musulmi da su gudanar da bukukuwan Karamar Sallah, cikin annashuwa.

Sannan yar doke da su ci gaba da yi wa jihar addu’ar samun ci gaba da dorewar zaman lafiya da karuwar arziki mai yalwa.