✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sallah: Yadda kasuwannin Kano 6 suka cika makil —Rahoto

Yadda jama'a ke cefanen sallah a manyan kasuwannin Kano shida.

A yayin da Karamar Sallah ta kawo jiki, kasuwannin Kano sun kasance babu masakar tsinke da mutane daga sassan Najeriya da ke ta kokarin sayen abubuwan da za su yi amfani da su da sallar. 

A yayin da Sarkin Musulmi ya bukaci a fara neman watan Karamar Sallar daga ranar Talata, gabanin sallar idi a ranar Laraba ko Alhamis, Aminiya ta lura tun ranar Litinin manyan kasuwanni shida na Jihar suka zama babu masaka tsinke.

Kano cibiya ce ta hada-hadar kasuwanci da kuma bude ido yayin bukukuwan Sallah, amma a Karamar Sallar bara, an takaita zirga-zigar mutane a irin wanna lokaci, musamman masu shigowa jihar, saboda annobar COVID-19.

A kan haka ne muka yi duba kan wainar da ake toyawa a kasuwannin Jihar a jajibirin Karamar Sallar wannan shekara.

A ziyarar da Aminiya ta kai Kasuwar Singa, wadda ta shahara wajen sayar da kayan abinci, al’amarin sai wanda ya gani.

Mun samu labarin tun a ranar Litinin dubun dubatar mutane suka yi wa kasuwar tsinke domin yin cefanen sallah.

A Kasuwar Sabon Gari, wadda ta yi fice wajen harkar kayayyakin amfanin yau da kullum, abin ba dama.

Duk inda ka duba, mutane ne bila-adadin suke kai-komon nema da cinikin kayan kawa da za su yi amfani da su a lokacin bikin.

Aminiya ta leka Kasuwar Kwari, wadda ta shahara wajen sayar da tufafi, inda ta iske dubun dubatar mutane suna ta zarya domin sayen kayan sallah, ’yan kanti da kuma kayan yari.

Wakilinmu ya gano cea tun a ranar Litinin kasuwar, ta cika ta batsa da dan Adam, saboda kara matsowar Salla.

Kazalika irin cikowar mutane da aka samu a kan titin IBB da ke kusa da kasuwar, zuwa abbatuwa har zuwa Kofar Wambai sai wanda ya gani.

Masu sayar da takalma da kayan kwalliya da sauransu, wato Kasuwar Wambai, abun sai wanda ya gani.

Dubban mutane, maza da mata ne suka yi dafifi, kowanne da abin da yake son saya da za su yi amfani da su a lokacin Sallar.

A bangaren kayan miya da kayan da na sarrafa kayan abinci kuwa, Kasuwar ’Yan Kaba ce kan gaba.

Aminiya ta lura cewa tun a ranar Litinin lamarin kasuwar ya zama babu dama, inda mutane suka yi mata cikar farar dango wajen cifanen kayan miya, kaji, nama da dangoginsu na abincin sallah.

Kasuwar Dawanau kuwa, a nahiyar Afirka ma ta yi shuhura wajen sayar da hatsi.

Aminiya ta ziyarci Kasuwar inda ta iske cincirindon mutane na hada-hadar tsabar kayan abinci.

Wasu mutanen sun fi mayar da hankali ne waje sayen hatsin da za su fitar da Zakkar Ko da kuma wanda za su yi tuwon sallah da shi.