Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta raba wa mambobinta shanu 400 don gudanar da shagalin bikin Karamar Sallah.
Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na Jihar, Lawal Liman ya ce tsohon gwamna kuma jagoran Jam’iyyar a Jihar, Abdul’aziz Yari Abubakar ne ya bayar da shanun a raba wa ’ya’yan Jam’iyyar a fadin Jihar.
- Rashin tsaro: Addu’o’in da za a yi a Ramadan —Sarkin Musulmi
- Mahara sun kashe ’yan sanda sun kona caji ofis
Liman ya yaba da gudunmawar shanun wandan iyayen Jam’iyya a Kananan Hukumomi 14 da ke fadin Jihar kowanensu zai rabauta da shanu biyu.
Iyayen Jam’iyyar a matakin mazabu 147 kuma za su amfana da shanu biyu kowanensu.
“Sauran wadanda suka amfana da rabon sun hada da mata da kungiyoyin matasa da iyayen jam’iyya da masu unguwanni da dagatai da shugabannin addinai da kuma shugabannin Jam’iyya da ke fadin Jihar,” A cewarsa.
Shugaban ya ce, yanzu haka ana tsaka da gudanar da rabon shanun wanda tuni an kammala da Kananan Hukumomi tara wanda kwamitin da Kwamishina a Hukumar Kidaya ta Kasa, Muhammad Muttaka-Rini ke jagoranta.
“Har ila-yau muna gidiya da farin ciki bisa goyon baya da karfafa gwiwar ’yan jam’iyya da kyautata musu da yake,” inji Liman.
A karshe ya yi kira da ‘yan uwa musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na azumin Ramadan da su rokawa jihar da kasa Najeriya zaman lafiya.
A wani rahoto na baya-bayan nan an rawaito tsohon gwamnan ya yi rabon kayan abinci tirela 130,000 ga mutanen Jihar don yin buda-bakin azumi.