Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta cafke ɓata-gari 104 da ake zargi da aikata laifuka a wurare daban-daban a lokacin bukukuwan Sallah a faɗin jihar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Usaini Gumel ne, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), inda ya ce rundunar ta kama waɗanda ake zargin da muggan makamai a lokacin bukukuwan sallar da aka kammala.
- Shari’ar Hafsat Chuchu: Kotu ta sallami mai wankan gawar Nafiu
- Ba na son zama uban gidan kowa a siyasar Kaduna — El-Rufai
Gumel, ya ce rundunar na ci gaba da farautar ɓata-gari da nufin samar da zaman lafiya a jihar.
Ya bayyana cewa rundunar ta samar da matakan tsaro don tabbatar da zaman lafiya a yayin bukukuwan sallah.
“Mun fito da tsarin kamawa tare da gurfanar da duk wani mutum ko gungun mutanen da suka yi shirin tada tarzoma a jihar.”
Kwamishinan ya ce rundunar ta sanya ido musamman a wuraren da matasa ke taruwa a yayin bukukuwan sallah domin dakile munanan ayyuka.
Kwamishinan, ya kara da cewa “Yanzu haka muna shirin gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.”
Idan ba a manta ba jihar na fama da faɗace-faɗacen daba a baya-bayan nan, lamarin da ya yi sanadin salwantar ran wani matashi a unguwar Ɗorayi a jihar.