✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sallah: An baza jami’an KAROTA 1,000 a kan titunan Kano

Akwai tarar N15,000 ga duk wanda aka kama ya karya dokar hanya.

Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA, ta sanar da girke jami’anta 1,000 a kan titunan da ke fadin jihar, a  wani yunkuri na rage cunkoson ababen hawa yayin bukukuwan sallah.

Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Nabilusi Abubakar ya fitar a ranar Talata.

“Manajan Daraktan Hukumar KAROTA, Dokta Baffa Babba DanAgundi, ya gargadi iyayen yara da su guji ba wa yara kanana ababen hawa a yayin bukukuwan sallah.

“Sannan ana jan hankalin masu tuka ababen hawa da su guji karya dokokin hanya a yayin tuki, don gujewa asarar dukiya ko ta rayuka,” a cewar Abubakar.

Sanarwar ta ce, “KAROTA, ta umarci jami’anta da su sanya idanu wajen tabbatar da masu ababen hawa sun bi dokokin hanya a lokutan bukukuwan sallar da za a gudanar.

“Hukumar tana tunatar da jama’a cewar karya dokokin tuki a jihar, ya saba da sashe na 16 (4, 7 da 8) l, karkashin sakin layi na 12 na hukumar KAROTA na shekarar 2012, wanda aka tanadi tarar N15,000 ga duk wanda aka kama ya aikata hakan.

“Kazalika, duk wanda aka kama mai karancin shekaru na tuka babur mai kafa uku, wanda aka fi sani da Adaidaita sahu, za a ci sa tarar N20,000, sakamakon karya dokar sashe na 16 (4, 7 da 8) karkashin sakin layi na 2 da 3 na kundin laifuka na KAROTA, na shekarar 2012.”