✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Salgado ya zama Mataimakin Kocin Masar

Tsohon dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen, Michel Salgado ya zama Mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta Masar.  Ke nan yana daga…

Tsohon dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen, Michel Salgado ya zama Mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta Masar.  Ke nan yana daga cikin kocin da za su rika horar da ’yan kwallon Masar ciki har da Mohammed Salah na kulob din Liberpool.

 dan shekara 42  Salgado da Hary Ramzy ne za su rika taimaka wa kocin Masar Jabier Aguirre dan asalin Meziko.

Rahotanni sun ce tuni Salgado da takwarorinsa suka isa Masar don tunkarar wasan da Masar za ta yi da kasar Nijar  a gasar neman hayewa gasar cin Kofin Afirka da za a yi a Kamaru a 2019.

Michel Salgado ya taba buga wa kulob din Celta-bigo da Real Madrid na Sifen da kuma Blackburn Robers na Ingila kwallo kafin ya yi ritaya.  A lokacin da yake yi wa Madrid kwallo, ya yi wasa har sau 250.  Sannan ya yi wa kasar Sifen wasanni sau 53.

Ya yi wasa a Real Madrid ne a tsakanin 1999 zuwa 2009, daga nan ya koma kulobd in Blackburn Robers na Ingila a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2012 kafin ya yi ritaya.