✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Salah ya sabunta kwantaragin ci gaba da zama a Liverpool

Zaman Salah zai kara karfafa gwiwar magoya bayan Liverpool.

Mohamed Salah ya saka hannu kan kwantaragin ci gaba da taka leda a Liverpool kaka uku.

Saura kaka daya kwantiragin dan wasan mai shekara 30 ya kare a Anfield, daga baya aka kama rade-rade kan makomarsa a Liverpool.

Salah wanda dan kwallon tawagar Masar ne ya ci kwallo 156 a wasa 256 da ya yi wa Liverpool a kaka biyar da ya yi a Anfield, tun bayan da ya koma kungiyar daga Roma.

Bayanai sun ce sabuwar yarjejejeniyar da Salah ya kulla ya zama dan kwallon da zai ke karbar albashi mafi tsoka a tarihin kungiyar.

Salah ya lashe Kofin Zakarun Turai da Firimiyar Ingila da Kofin kalubale na FA Cup da League Cup da Fifa Club World Cup da kuma UEFA Super Cup a kungiyar Anfield.

Haka kuma ya lashe takalmin zinare uku a Firimiyar Ingila da ake kira Golden Boots, an kuma zabi dan wasan karo uku a matsayin dan wasa mafi kwazo karo biyu.

Wannan sa hannu da Salah ya yi zai kara karfafa gwiwar magoya bayan Liverpool, bayan da Sadio Mane ya koma Bayern Munich a bana.