✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakonnin ‘yan makaranta

A wannan makon ’yan makaranta  ne suka tofa albarkacin bakinsu, wasu kan darusssan d amuka gudanar, wasu kuwa tsokaci ne game da harkokin rayuwar al’umma.…

A wannan makon ’yan makaranta  ne suka tofa albarkacin bakinsu, wasu kan darusssan d amuka gudanar, wasu kuwa tsokaci ne game da harkokin rayuwar al’umma. Sannan masu koyon watsatttswake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya sun smao HOLAMAR YARJEJENIYAR SAYEN Amintacciyar Jarida cikin rahusa. Kuma za su kulla wata yarjejeniya da Sarkin Kasuwar Kamfanin buga amintattun jaridun kasar Haurobiya.
’Yan makaranta a kara kaimi, kada a makara. Ga batutuwanku nan na jero. Mu sha karatu cikin lumana.

Holamar samun rahusar jaridarmu
Assalamu alaikum daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido da ke cikin amintattar jaridar Haurobiya da ke Haurubja. Ina kira da daukacin al’ummar Haurobiya  da ma na ketare. A madadin makaranta muna sanar da tsofaffin dalibai dama sababbi cewa, akwai  HOLAMA mai zayyanar yarjejeniyar sayen JARIDARMU a farashi mai RAHUSA. Domin samun amintacciyar jarida cikin sauki kuma za a kaima duk inda ka/kike ko a birnin Lantsandan ne, indai kana cikin dalibai. Kuma muna bai wa dalibai na damo wajen rashin ganin sakonninsu akai-akai, kuma duk dalibin da yake da sako ya tuntubi shagaban makaranta ko jami’in hulda da jama’a.
Daga Aliyu Mukhtar Sa’idu Jami’in hulda da Jama’a  na kasa 08034332200, 09039332200.

Shelar cincirindo
Assalamu alaikum ‘yan uwa da abokan arziki masu ta’ammali da wannan shafi mai albarka na Dodorido, muna sanar da daliban makarantar Dodorido na Jihar Tumbin Giwa cincirindon dalibai da za a yi a  gudanar a KWALEJIN GWAMNA kusa da gidan Marigayi Babban mutum mai rawani na Birnin Dabo, ko in ce kasa da ta birin Baba-ojo dab da AKWATIN MAGANAR     Mai dan dago-dago. Ranar Lahadi:  Manuniyar sama ga watan Marisar shekara ta dubu karamin lauje da sili d amanuniyar sama,  da misalin karfe kofar hanci da rabi na yamma. Mai-duka ya ba da ikon zuwa ba tare da an zurare baa min.
Daga  Jami’in hulda da jama’a na kasa Aliyu Mukhtar Sa’idu 08034332200.

Gwarzon gwaraza
Assalamun alaikum da fatan alkhairi ga daukacin ma’abota  wannan shafi na makarantar Dodorido da ke cikin Amintacciyar jarida . iIna taya Direban allin wannan makaranta murnar lambar yabo da ya samu. Ai ba zancen kuri’a ba, dama ya cancanci hakan in kuka duba  irin da kokarin tsage mai uwar fada  (dokin karfe),  har  ma sabon yare ya samar wa al’ummar wannan sararin subhanar. Kamata ya yi jam’in jami’o’in kasar Haurobiya su fara nazarin wannan hamshakin yaren,  musamman Jami’ar Tumbin Giwa.  Tunda  duk mai yaren Hau-hau masu hawan sa ba tare da sa-in-sa ba suna takama da ita! Na gode.
Daga: Idris  Muhammad  Musa (FASAHA COMMUNICATION) Bachi-rauwa shatalen Ungo-da-gwagwo Jihar Tumbin Giwa  08065467711. [email protected]

Shawara ga al’umma
Sallama ga masu kadaita Mahalicci a duk inda suke, ga wasu shawarwari guda babban lauje kamar haka:-
1. Ilimi: shi ne farkon abin da zai gyara al’amura. Don haka sai a dage wajen nemansa da yin aiki da shi.
2. Hadin kai: matasa su fara tunanin yin ‘’merger’’ (watau Hadaka) ta kungiyoyi da ake da su; a samu kadan masu kwari, masu nagarta, wadanda za su iya tsinana wani abu. kungiyar Jama’a Islami ta Indonesia ta isa misali: a fannin ilimi, ta samarwa da kasar Jami’ah dari tsayuwa bisa ksafa daya; a fannin lafiya, ta na da farfajiyar Bokan Turai a loko da sako na kasar; ita take tsara aikin hajji ga mafi yawan ’yan kasar – ta yi musu adashin gata, ta hayi jiragen sama, ta tanadi masaukai, da motoci, da abinci; akwai bukatar samarwa da  Masu fuskantar alkibla irin wadannan managartan dabaru.
3. Matasa su rika daukar wata koyarwa  ta fuskantar alkibla don kadaita Mahalicci da ibada su dabbakata a shekara; misali: gaskiya, kula da lokaci, cika alkawari, tsabta, bin ka’ida, sallah a jam’i, ko ma saka hula; bayan shekara, sai a sake daukar wani; kafin shekara goma sai an kayar da duk matsalolin da suke damun mu, kamar yadda ya faru a kasashe da dama;
4. Riko da sana’a ko yaya take; banda zaman kshe fatari
5. Zaben mutane na gari a kowane mataki. godiya mai yawa ga Mahalicinmu baki sili.
Daga: dalibin makarantar Jihar dakin -kara, Sani Yaro Muhammad 07037881271

Jaje ga al’ummar Tumbin-giwa
Assalamu alaikum al’ummar Jihar -Tumbin giwa ina jajentawa bisa iftila’in gobarar wutar da ya shafi ‘yan kasuwar Singa da kasuwar Kurmi  da ke cikin kwaryar cikin garin Birnin Dabo. Mai duka ya kara kare gaba.
Daga dalbin Makaranta  Bashir A. Musa 08031396787.

Assalamullaahi Alaikum. Na san Haurobiyawa na cike da kawa-zucin ganin abubuwan masarufi sun wadata a kowanne lungu da sako na Haurobiya. Amma batu na dokin karfe muna da bukatar mu dan tsahirta wa shugaban masu Burin-huriyya ya bi wadannan batutuwa daga-daga.
Kada mu ce za mu yi gaggawa domin akan ce mana aikin iblisu ne babban magabcin mu. Ya kamata mu fahimci cewa, a hankali ake dirar wa matsalolin da suke addabar Haurobiyawan Kudanci da Arewacin kasar nan don a dauki izina.
Dubi yadda ‘yan tada zaune tsayen Hauren Danja da masu Bobo da kwambon bokoko ke neman zama tarihi. Dubi yadda kasar ke tafiya duk da matsin tattalin arziki da faduwar darajar farashi na tunkuza.
Ni dai har yanzu ina goyon bayan yadda dogon mutumin nan na Birnin Dikko ke jan akalar rakumin dawa da na gidan Haurobiyawa, musamman kafewa da ya yi a kan ba zai karya darajar Hauro ba, Domin bai ga alfanun hakan ba. Wannan ne kuma tunanin duk wanda ya je gano ya rutsa gwano a cikin kwano.
Daga Ashiru danazumi Gwarzo. [email protected] 07036589807.