✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakonnin Fadar FDk

  Tsokaci   Fatan alheri ga FDk. A gaskiya ina da tsokaci ga masoya. Abin da nake so na ce kuwa shi ne, ya kamata…

 

Tsokaci

 

Fatan alheri ga FDk. A gaskiya ina da tsokaci ga masoya. Abin da nake so na ce kuwa shi ne, ya kamata duk wani masoyi ya natsu wajen zabar abar kaunarsa, domin wani lokacin mukan yi gaugawa wajen zaben masoyi ko masoyiya. Hakan yakan sa mutum ya yi zaben tumun dare, haka ya sa za ka ga an yi aure watanni kadan sai ka ga auren ya mutu, an rasa kan matsalar. Mazan ne ko matan? Da fatan za mu natsu wajen zaben daidai da mu. 

Daga Nura S. A. Jigawa

 

Gargadi ga maza

FDk, a gaskiya maza mafi yawanmu wallahi ba mu da amana, saboda kai ne yau za ka ce kana son mace, tun ba ta amince maka ba har ka fi karfinta ta amince da soyayyarka kuma ta so ka fiye da son da kake mata. Amma da namiji ya fahimci cewa ta dauki soyayyarta gaba daya ta damka masa, to daga nan za ka ga wulakanci na biyowa baya, domin lokacin ta riga ta raja’a a kansa; daga nan sai yaudara ta biyo baya, daga nan ya yi gaba ya bar ta da wannan tabon. Don haka, don Allah mu ji tsoron Allah, mu daina yaudarar masoyanmu, mu tuna da mutuwa da kuma cewa duk abin da ka yi wa ’yar wani to za a yi wa taka.

Daga Muhammad Hassan danbaza, (07068040761)

 

Neman shawara

FDk, da fatan kana lafiya, albishirinku ’yan majalisar Dausayin kauna, ina so in shaida maku cewa na samu babbar masoyiya mai suna Maryam. Ina da hawan jini amma da haduwarmu da ita, irin yadda take kwantar mani hankali abin ya wuce misali. Kai saboda soyayyarmu ta yi nisa, Gimbiya nake kiranta saboda kunyar kiran sunanta. Amma kash, yayana ya danna mani jan kati, inda yanzu haka yana so ya hada ni da wata yarinya kodayake wannan ba ya rasa nasaba da abin da iyayen Maryam suka fada; cewa sai na bar Fatakwal zan auri Gimbiya Maryam. Shi ya sa yayana ya dauki matakin hada ni da Hauwa’u, wada take cewa ko’ina nake a duniya za ta bi ni. Ku ba ni shawara.

Daga Alkassim Yola (08144535310)

 

Fatan Alheri Daga Fadar FDk:

1-Mahmud M. Rabi’u Fatakwal (08140645275).

2-Khalifa Jibirin Gombe.

3-Bala Oil Royal Dream Maraba (07086361212).

4-Sani Isyaku Danja-Kano (08069037983).

5-Hadiza Ya’u Funtuwa.

6-Hussain danjari Umar Kadarko (08038810162).

7-dahiru Sunusi Mangal (08039500115).

8-Abu Sani Katsina,

9-Mika’ilu Idris Kusallah (08132752275).

10-Saifullahi (Saif) Ningi.

11-Shehu Akar Kiyawa Jigawa.

12-Muhmmd Idris bn Salihi Abuja.

13-Abdurrazak Saleh Inuwa (08032117371).

14-Murtala Ahmed Abubakar Kwalli (07068295953).

15-Bahijja Yusuf dorayi Kano.

16-Abdulhamidu Gwangwan Rogo (07013300079).

17-Usaini Isma Eel Nasarawa Jahun-Bauchi.