✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakonni:

Adon gari ban da kurungu Bayan salama irin ta masu kadaita Mahallici sili, ina jin-jina ga daliban wannan makaranta tamu sili a fadin kasar Haurobiya.…

Adon gari ban da kurungu

Bayan salama irin ta masu kadaita Mahallici sili, ina jin-jina ga daliban wannan makaranta tamu sili a fadin kasar Haurobiya. Ina rokon Mai-duka ya yi jagoran wannan jarida da ake bugawa a babban birnin Haurobya.Kuma ina kira ga manya-manyan iyayen giji wajen nunawa kana na hanya mai dorewa dodar. Abin da yake ba ni mamaki shi ne a duk lokacin da aka ce ka ga ’yar dugwi-dugwi kana so da niyar assasa sunar Ma’aikin Mai-duka, sai ka ga ‘yar budurwa ta dauki katon rawani, wanda ba za ta iya war-ware shi, wata kuma da ka furta mata haka ka ga zumudi ba zama kamar ta ci kafar zomo, ta yi ta zagaya wajen kawaye sai zuba wane saurayi na. ina kira ga iyaye da su kula da ‘ya’yansu don ba su ingantacciyar tarbiyya da su rika sa su don rage burika don wanyewa da gobe lafiya, kurungu ba kyau, iyayen giji hattara dai, in dai saurayi da gaske yake a yi masa na jarirai, don kada ya zuke ya zarce gari mai sunan lawurje ko ma  ya tafi kasar Bara-zana-da-zilliya.
 Muhammad I. Abubakar Minjibir dalibin Jihar Tumbin Giwa 08035997648

Gidan Bokan Turai
Assalamu alaikum daliban wannan makaranta ta mu mai albarka ta Dodorido, wadda shafinta  yake cikin Amintattar jarida, wadda ake bugawa a Harubaja babban birnin Haurobiya. Nashe-i-sasshe wani rukuni ne na ‘yan kwadago da gwamnatin Haurobiya ta jadadda shi a cikin shekara ta alif sili da manuniyar kasa da manuniyar kasa da manuniyar kasa a cikin tsarin kwance tushe na kasa. Wannan tsari ya ta’allaka ne akan shi dan kwadon da matarsa da ‘yan dugwi-dugwin shekarun su bai gaza sili da madambaci ba kuma tsayuwa bisa kafa daya rak ka ji fa.
Zance na dokin karfe duk wani dan kwadago a kasar Haurobiya ya kwana ya tashi ba abin da ta yake girgiza ni shi ne makomarsa idan ya gama aiki. Bayan haka sanin kowa ne uwar jiki ita ce kan gaba, domin ko kana kwadagon ko yanzu aka dauke idan baka da isasshiyar uwar jiki sai a ce waje road. Idan mun koma gidan Bokan Turai a can ne ake zabtare wa dukkan wani dan kwadago wani kaso da Allah-ba-ni-in-biya-bashi don kulawa da uwar jikinsa, sai dai ba an gizon yake saka ba. Idan ka sami wata tawaya da kaje wajen Bokan Turai ya caje ciki da waje idan ya yima watsatstsaken magunguna don kaje ka saya a wajen Fama-da-chi sai suce basu da wasu irin nau in magungunan wai don suna da damin Hauro da yawa Allah sarki ‘yan kwadagon Haurobiya kaji, kai wannan kungiya ta Nashe-i-sasshe ko suna da masaniyar wannan al’amura irin na waskiya da ake yi a fama-da-chi ko kuma Nashe-i-sashe shi ne yake lashe dukan irin wannan magunguna masu damin Hauro mai nauyi. In ta kaita muku annan zance na dokin karfe idan ake mayi-magi har damin Hauronsa ya kai sili da zage,zage da zagaye ko sama da haka to lallai sai dai mara uwar jikin nan jikinsa ya gaya masa, ko kuma ya zagaya gidajen Bokan Turan da suke da su idan har ka ce to tunda babu ya za a yi, sai su je ka je can hattama idan kaje don a yi ma gwaje-gwaje, sai a ce ma irin wannan gwajin ba ya cikin tsari. Wayyo! Wayyo! Wayyo!  ‘yan kwadagon
Haurobiya ta, shin ko kungiyar kwadago ta kasa indai ba ta sha kasa ta san da irin wannan kama karya da akewa ‘ya ‘yanta a gidajen bokan turai. idan baha  kuma ba, yana da kyau a canja wannan tsari na Nashe-i-Sasshe don kowanne dan kwadago ya ji nashe-nashe a hannunsa, don lokuta da dama gidajen Bokan Turai a kasar nan ta Haurobiya, sukan daka yaji mai dan karen zafi, wanda har sai Baba tagani. Wannan ya kansa ’yan kwadago su shiga rudani ba ji, ba gani tunda irin wannan tsari baya zuwa hannunsu, bugu da kari, kuma idan larura ta zo wa mutum a farkon wata haka shi ma zai shiga fangan-fangan, tunda an biya shi, ya biya bashi ka ga maganar larura idan ta zo, sai dai ya kara nauyin bashi ko kuma larura ta kai shi kasa wan-war Mai-duka ya yi mana dauki a wannan bangare.
Daga: Aliyu Mukhtar Sa’du Jami’in hulda da Jama’a na kasa 08034332200 /09039332200.

Ta’aziyya
Inna lillahi wa ‘inna ilaihir raju’un, dukkan mai numfashi zai dandana mutuwa. Muna sanar da al’umma masu kallon alkibla rasuwar Hajiya Zainab Sulaiman, ranar sili da manuniyar sama wanda ya yi daidai da watan kwanciyar magirbi na wannan shekara. Marigayiyar, ita ce  kakar dalibar wannan makaranta tamu ta Dodorido,  Khadija Abubakar Sadik, a garin masu Zare, zare, reshen Jihar Bau-bnawan-cici. Ga lambar kurtun nan ga mai son yi mata ta’aziyya. 08135670493. Mai-duka ya yi mata rahama, ya sa aljanna ce makoma. Mu kuma ya kyautata namu karshen. Kowa ya ce amin!

A lullube jiki
Assalamu alaikum bayan sallama da salama ga daukacin daliban wannan makaranta ta mu mai albarka ta Dodorido. Zance na dokin karfe ba batun waskiya ba Arewata mun fara sakin al’adu dama suran al’amura namu a yau da kullum, domin a kullum idan na tashi ba abin da nake fara dubawa a cikin al’umma, face ya nayin sa suturar malam hau-hau a yau. Idan muka yi waiwaye a shekarun da suka arce ba haka Malam Hau-hau yake da na yanzu ba. Duba da yadda ‘yan dugwi-dugwi da ma iyayensu suke saka kan gida yanayin suturasa ba ta wuce kananan kaya ba. Haka yaransa, maimakon ya rika sa shakwara da jamfa, wadda ko da an jefe shi, ba zai same shi ba ko ya rika ta ammali da babbar riga, wadda za ka rika riga kowa a kowanne al’amura na yau da kullum. Haka ma yaransa za su kasance in dai ya saba masu. Idan aka yi duba da wajen kallon alkibla a dakin Mai-duka sai ka ga mai jan sikiyarin sallah da wata ’yar  dangalalar riga, wadda ni a tunani na bai kamata a ce shagaba a wajen kallan alkibla da irin wannan ba.
bangaren iyayen giji wannan zan iya cewa da sauran kallo makwabcin mai akuya ya sai kura, yawa-yawan ‘yan matan yanzu da ma iyayensu, ba su fiye sa suturar da za ta rufe jikinsu daga sama zawa kasa ba, a da nasan koda sa hijabi bai bazu a kasar Hau-hau ba, musamman ma Arewatawa. Ni nasan mutanen gabashiyar Haurobiya an sansu da sa wani katon mayafi,  mai suna ta zaga, wanda yake zagaye dukkan jikin mace, wadda a wannan zamani ba haka yake ba. Abin ban haushi ma, za ka ga mace da ta fara haihuwa idan za ta fita unguwa, sai ka ga ta dan yafa mayafi dan figil-figil, maraba da shaidan, ko dan kil din hijabi, wato mu-sulmiya ke nan Idan fa ta sa wannan kayan sai su tattare shi, a makale shi a wuya, bayan ko oho, wanda wannan shi yake nuna wa shaidanun mutane da aljanu gurbin zama, hatta masu daura dan kwali, abin ba haka yake a da ba, don a wancan lokacin mace tana da dan kwali, yanzu kuwa kai ya kwaile, tunda har wata hula mata ke sawa dan zamananci, wanda a cikin gida ba a damu da suturta kai ba.
Daga: Gimbiya Halima Shehu Shagamu 08038425171.   

Shelar taro
Assalamu alaikum. Ya jama’ar Jihar Tumbin giwa, maza da mata, muna sanar da ku taron daliban makarantar Dodorido. Kamar yadda aka saba yi a cikin karamar Kukumar cibiyar tumbin giwa. A kwanar gaban gari, makarantar Sheik Musa Ali Islamic Foundation, jibi ranar da aka haifi danladi da misalin karfe kofar hanci da kofar hanci da zagaye na yammacin ranar. Daga Jami’in hulda da jama’a na jiha, Umar Muhammad Abdullahi  08067676454.

Bishiyar shan inuwar adon gari
Sallama  a gareku daliban wannan makaranta ta Dodorido da kuma ‘ya uwana inuwar adon gari a duk inda suke. ‘yan uwa kar ku manta, ku ne fa bishiyoyi ga a don gari, a duk inda kuke, dole ku  a ka garkamawa ragamar adon gari, ku zama inuwa mai sanyi a garesu mai ciresu daga dukkan gawayin uwar hanji, wanda in da baku, rayuwarsu takan ciwata. Haka kuma in ba su rayuwarku takan zama kwai mai jini, amma fa an yi walkiya na hango da yawanku ba kwa zama masu inuwa mai sanyi, musamman in da ba a kashin awaki kuke ba, wato an daura igiya a tsakani. Anyi wal-wal na walko da yawanku a cikin walkiya, basa hubbanta wa a don gari, sai da na goro a cikin miya. Yawancinku sai adon gari ta yarda a ha’ince ta, ko da shan shanci ne, sannan za a habanta mata, komai daurin gwarmai da take fuskanta, in ba ta bada hadin goruba ba, babu bishiyar da zai tausaya mata, ko da katin kurtun magana ne, na wasko duk adon garin da take fandam-fandam a inuwar bishiyu, tabbas ta mika goruba a ‘balisu iblis’ ya dare ya yi sansani, a nan za ka ganta da manyan kara kunne, shorido taya tsayuwa, bisa kafa daya, shafe jiki saka. Mu ji tsoron Mai-duka, mu habanta musu don Mai-duka, ba don Mai-duka ya baku, ku ba mu ba. Mu tuna manyan gobe namu in za mu gamsu a wannan rayuwar ya za mu yi? Mu gane in za mu bata adon garin wasu, sai an bata namu. Ni kaina  na sha korar bishiyu masu damuna, ta hanyar cewa su turo min da katin kurtun magana, sai ka ji shiru, kamar malam ya ci shirwa.
Daga Hafsat Kurna,  Jihar Tumbin giwa 07032138614.