Attajirin duniya, Bill Gates ya sallama wa matarsa, Melinda Dala biliyan 127 na dukiyarsa saboda sakin ta da ya yi.
Rabuwar auren shekara 27 tsakanin Bill —mutum mafi arziki na hudu a duniya— da Melinda shi wanda aka ba da dukiya mafi yawa don sallamar matar da ta rabu da mijinta a duniya.
- An kama matashi da sassan jikin dan Adam
- An kama ’yan damfara masu kwaikwayon muryar aljanu a Katsina
Ga wasu attajiran duniya da matansu suka fi samun biliyoyin daloli sakamakon rabuwar auren nasu.
- Jeff Bezos – $38bn
Kafin Bill da Melinda, mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos shi ne mutumin da ya fi ba da kudi mafi yawa ga matar da ya rabu da ita a duniya.
A lokacin rabuwar Jeff Bezo da matarsa, MacKenzie Scott da suka shekara 25 tare a 2019, ya ba ta Dala bilyan 38.
Yanzu MacKenzie ita ce ta uku a jerin mata mafiya arziki a duniya, kuma kimar kadarorinta ta kai Dala biliyan 6.1, shi kuma Jeff shi ne mutum mafi yawan tarin dukiya duniya.
- Rupert Murdoch – $1.8bn
A 1999 attajiri mai kamfanin yada labarai, Rupert Murdoch, ya saki matarsa ta biyu, Anna Maria Mann bayan sun haifi ’ya’ya uku.
A lokacin, Rupert ya sallama wa Murdoch kadarorinsa na Dala biliyan 1.7 da kuma tsabar kudi Dala miliyan 110.
- Chey Tae-won – $1.6bn
Rabuwar auren Chey Tea-won da Roh Soh-yeong, wanda kafafen yada labarai suka yi wa lakabi da Sakin Karni ya lakume Dala biliyan 1.6.
Dukiyar da Chey ya mallaka wa Roh (wadda ’yar tsohon Janar din soja ce), ta kai kashi 42.3% na karfin jarin kamfaninsa na SK Holdings Co.
Chey Tea-won shi ne shugaban SK Group, wanda shi ne kamfani na uku mafi girma a kasar Koriya ta Kudu.
- Tiger Woods – $710m
Fitaccen dan wasan kwallon Golf na duniya, Tiger Woods ya sallama kadarorin Dala miliyan 710 ga tsohuwar matarsa, Elin Nordegren bayan mutuwar aurensu.
Woods da Elin Nordegren sun rabu a 2010 bayan shekara shida suna tare ta kuma haifa masa ’ya’ya biyu.
- Michael Jordan – $168m
Shahararen dan wasan kwallon kwando na duniya, Michael Jordan, ya sallama wa Juanita Vanoy, Dala miliyan 168 bayan rabuwar aurensu a 2006.
A lokacin, Juanita ta zama ita ce matar da ta samu dukiyar sallamar rabuwar aure mafi yawa a duniya.
- Harrison Ford – $118m
A 2004 tauraron fina-fina Hollywood, Harrison Ford ya mallaka wa matarsa, marigayiya Melissa Mathison Dala miliyan 118 bayan sun rabu.
Harrison da Mellissa Mathison suna da ’ya’ya biyu, mace da na miji kafin rabuwarsu.
- Song Joong-ki da Song Hye-kyo – $86.5m
Rabuwar auren taurarin fitaccen fim din Descendants of the Sun, Song Joong-ki da Song Hye-kyo ’yan kasar Koriya ta Kudu na daga cikin wadanda suka fi daukar hankali a nahiyar Asiya.
Amma duk da rabuwarsu, maimakon sallama wa matar kadarori, sun ci gaba da tarayya a mallakar dukiyar da kimarta ta kai Dala miliyan 86.5.
Song da Song na daga cikin taurarin masu albashi mafi tsoka a matsayinsu na jaruman fitaccen wasan kwaikwayon.