✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bill Gates, Dangote sun gana da Shettima da Gwamnoni a Aso Rock

Yayin taron an tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tattalin arziƙin Najeriya.

Shahararren Attajirin Amurka, Bill Gates da Shugaban Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, sun ziyarci Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Sun gana da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, kafin taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) da aka gudanar a ɗakin taro na Aso Rock.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Hope Uzodimma daga Jihar Imo, Babagana Umara Zulum daga Jihar Borno, Bala Mohammed daga Jihar Bauchi.

Sauran sun haɗa da Abdullahi Sule daga Jihar Nasarawa, Duoye Diri daga Bayelsa, Francis Nwifuru daga Ebonyi, da Lawal Dauda daga Zamfara.

Wasu daga cikin ministoci da mataimakan gwamnoni sun wakilci jihohinsu a yayin taron.

NEC, wani kwamiti ne da ke bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan al’amuran tattalin arziƙi.

Daga cikin mambobin kwamitin akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa, gwamnonin jihohi 36, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Ministan Kuɗi, da wasu manyan jami’an tattalin arziƙi.

A taron NEC na baya-bayan nan, mambobin sun amince da naɗa gwamnonin jihohi guda shida a matsayin mambobin kwamitin Niger Delta Power Holding Company (NDPHC).

Waɗannan gwamnonin suna wakiltar yankuna shida na Najeriya da suka haɗa da jihohin Borno, Katsina, Imo, Ekiti, Kwara, da Akwa Ibom.

Wani bayani daga ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha ya sanya hannu, ya bayyana cewa NEC ta jaddada muhimmancin NDPHC wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa yayin da ta amince da naɗe-naɗen.

An kuma gabatar da sabbin bayanai da shawarwari a lokacin taron.