✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Sake fasalin Naira zai sa ’yan bindiga su koma karbar kudin fansa da Dalar Amurka’

Malamin ya ce sam dokar ba ta dace da lokaci ba

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce shirin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi na sauya fasalin Naira zai sa masu garkuwa da mutane su koma karbar Dalar Amurka a matsayin kudin fansa.

A ranar 26 ga watan Oktoba ce dai CBN ya bayyana cewa ya shirya sake fasalin wasu sabbin takardun kudi na Naira.

Babban bankin ya ce sabbin takardun sun hada da N200, N500 da N1000, inda ya kara da cewa sabon fasalin kudin zai fara aiki daga tsakiyar watan Disambar 2022.

Sai dai da yake mayar da martani kan lamarin, Sheikh Gumi, ya ce manufar ta zo ne a lokacin da bai dace ba kuma za ta jefa ’yan kasa cikin mawuyacin hali.

“Wannan lamarin zai dagula komai, zai kara sanya wa wadannan mutanen su koma neman Dala saboda suna cikin halin yunwa da matsi.

“Wannan ba lokacin da za a yi irin haka ba ne don zai karya tattalin arziki!

“Mutanen da ke sayar da kayayyaki fada maka yawancin ’yan Najeriya ba su da kudin sayen abubuwa; don haka yawancin ’yan kasuwa suna tafka asara ne. A wannan lokacin duk wani abu da zai haifar da tabarbarewar kudi zai zama bala’i ga al’umma.

“Yawancin kyawawan abubuwa ana bata su ne saboda rashin dacen lokaci. Wannan ma ya zo a lokacin da bai dace ba.

“Irin wannan shiri ba na gwamnatin da ke cikin halin kaka-ni-ka-yi ba ne, idan har akwai wata fa’ida a cikin irin wadannan abubuwan, yawanci yakan zo ne bayan shekaru da dama amma ba a cikin fama da talauci da wahalhalu wanda babu wata gwamnati mai kyakkyawar manufa da za ta kawo irin wannan zalunci ba.”