Shugaban Hukumar Yaki da Ci Hanci da Rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce akwai yiwuwar Dalar Amurka ta fadi zuwa N200 idan aka kammala aikin sake fasalin Naira.
Ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na Deutsche Welle (DW).
- Zan dora daga nasarorin Buhari idan na ci zabe – Tinubu
- Donald Trump ya kaddamar da takararsa ta sake neman Shugabancin Amurka
Abdulrasheed ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi abin a yaba masa saboda amincewa da bukatar sake fasalin Nairar da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zo da ita.
A cewarsa, “Doka ta ce a sauya fasalin takardun Naira bayan duk shekara takwas, amma mun yi shekara 20 ba tare da canza su ba.
“Hakan ya yi sanadiyar kasancewar kaso 85 cikin 100 na kudin kasar ba sa bankuna, sai Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zo da wannan shirin, inda a tashin farko Dala ta kai kusan N880, sannan daga baya ta fado kusan N680 ku kusa da haka.
“To ka ga idan aka kammala wannan sauya fasalin, wa ma ya sani, watakila Dala ta fadi zuwa N200,” inji shi.
Shugaban na EFCC ya kuma ce babu wata manufa ta siyasa a yunkurin sauya kudin, sannan ya yi kira ga ’yan Najeriya su kai rahoton duk wani mai boye kudi a gida.
“Wasu mutane sun sace kudaden jama’a sun boye su, shi ya sa muke so su kawo su cikin bankuna su ajiye.
“Muna ba ’yan Najeriya tabbacin cewa a shirye muke mu karbi rahoton duk wani wanda ake zargi da boye kudi, idan muka bincika kuma muka gano gaskiya ne, za mu ba shi kaso biyar cikin 100 na kudin,” inji Abdulrasheed Bawa.