✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakataren Gwamnatin Katsina ya dauki nauyin yi wa masu ciwon kunne 350 magani

A ranar Talatar da ta gabata ce aka kaddamar da shirin yi wa masu ciwon kunne magani kyauta a karamar Hukumar danmusa da ke Jihar…

A ranar Talatar da ta gabata ce aka kaddamar da shirin yi wa masu ciwon kunne magani kyauta a karamar Hukumar danmusa da ke Jihar Katsina, inda majinyata 350 za su amfana da shi da Sakataren Gwamnatin Jihar Dokta Mustafa Muhammad Inwa ya dauki nauyin aiwatar da shi domin tallafa wa marasa galihu. 

Daraktan Labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin wanda ya wakilci Sakataren ya ce, “Dokta Mustafa ya lura masu irin wannan matsalar a yankin masu karamin karfe ne, saboda haka ya dauko kwararrun likitoci a fannin ya kuma dauki nauyin aiwatar da komai na aikin domin tallafa wa wadannan bayin Allah ba tare da bambancin siyasa ba. Sakataren Gwamnatin tuni ya sanya an fito da masu matsalar karanci ji ko wadda ke da nasaba da ji daga mazabu 11 na karamar hukumar domin yi musu aiki kyauta. Saboda haka, ya umarce ni in yi kira ga wadanda za su amfana da shirin su zamo masu hakuri tare da bin umarnin da likitocin za su ba su.”

Dokta Mustafa ya ja hankalin jama’a su guji kwanciyar cinkosa wuri daya ko inda babu wadatacciray iska musamman a wannan lokaci na zafi. 

Magajin Malam kuma Hakimin danmusa, Alhaji Darda’u Ma’azu Abubakar gode wa Sakataren ya yi a kan wannan gudunmawa kasancewarsa na dan asalin wannan masarauta. Hakimin ya nuna jin dadinsa a kan tallafin musamman yadda aka janye batun siyasa wajen bayar da shi.

Shugaban Jam’iyyar APC a karamar hukumar, Alhaji Aminu Sani ya ce, an raba wadanda za a yi wa aikin zuwa gida uku domin samun saukin yi musu aikin. Kuma ya yi kira gare su da su ci gaba da bai wa gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Aminu Masari goyon baya domin aiwatar da ayyukan alheri ga al’ummar jihar.

Dokta Suleiman Abdulmajid wanda shi ne jagoran likitocin da za su aiwatar da aikin ya ce, za su yi wa masu kananan matsaloli aiki nan take tare da ba su magunguna yayin da masu manyan matsaloli za a yi musu aiki mataki-mataki.