✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘‘Sakacin shugabanni ya kawo rikicin Fulani da Hausawa a Legas’’

A shekranjiya Laraba ce jami’an tsaro suka yi wa kasuwar shanu ta Abbatuwa da ke Legas ƙawanya, bayan ɓarkewar wani rikici a tsaknin Fulani da…

A shekranjiya Laraba ce jami’an tsaro suka yi wa kasuwar shanu ta Abbatuwa da ke Legas ƙawanya, bayan ɓarkewar wani rikici a tsaknin Fulani da Hausawa a kasuwar, abin da wadansu ke kallon sabon abu ne.
Rikicin ya janyo salwantar rayuka da ɗimbin dukiyar jama’a, kuma ya hukuma ta rufe kasuwar.
A cewar wani matashi mai suna Adam da ke kasuwar, rikicin ya samo asali ne a yankin saman kwangiri na kasuwar, wajen da ke da yawan matasa ’yan shaye-shaye. “Wani Bafulatani ya yi tatil da giya, ya fito yana bugun jama’a sai mutanen yankin suka fusata suka far masa. Ko baya ga haka, masu shaye-shayen kan addabi jama’a da ƙwace wayoyin hannu da sanen kuɗi, bayan da gwamnati ta yi rusau a kasuwar, abin da ya sanya da yawansu suka rasa wajen kwana da wuraren gudanar da kasuwanci,”inji shi.
A cewar Garba, ɗan kasuwa a karar shanu: “Bayan da matasan Fulanin suka addabi jama’a da hare-hare ne sai wadansu suka kai ƙararsu ga shugabannin Fulanin kasuwar amma sai suka ce ai waɗannan Fulani ba a ƙarƙashinsu suke ba kuma ba su da iko a kansu. Da hare-haren suka yi tsamari sai matasa Hausawa, waɗanda yawancinsu ’yan gwangwan ne da ke zaune a saman kwangirin suka yi zuga suka far wa Fulanin da ke kai hare-haren. Da suka kora su suka gudu fadar Sarki, haka matasan suka rutsa su can suka farfasa duk motocin da ke wajen. Da gari ya waye sai Fulanin suka sake ɗamara, aka ci gaba da fafatawa, kafin jami’an tsaro su zo su shiga tsakani. An yi ɓarna kwarai, an kuma halaka aƙalla mutum 12, domin sai da aka shafe kwana uku ana rikicin,” inji shi.
A cewar Sarkin Shuwa-Arab na Legas, Alhaji Jibrin Yahaya, abin baƙin ciki ne da takaici a ce Fulani da Hausawa na rikici a tsakaninsu a Kurmi, abin na da alaƙa da sakacin shugabannin sassan biyu, domin tun gabanin lamarin ya yi ƙamari ya kamata a magance shi.
Shgaban ƙungiyar haɗin kan ’yan Arewa, Alhaji Ado Shu’aibu Ɗansudu, ya danganta rikicin da rashin haɗin kai na ’yan Arewa da raunin shugabannin kasuwar. “A nan ne za ka ga ƙungiyar ’yan Kebbi daban ta ’yan Sakkwato daban Kanawa ma da tasu, su ma Zazzagawa haka, to mene ne alfanun haka? Wajibi ne a samu shugabanci da zai kawar da matasa ’yan maye a kasuwar,” inji shi.