✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sai Lahadi za a ƙarasa zaɓen Legas – INEC

Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC ta ɗage zaɓen  gwamna da ɗan majalisar jiha a akwatuna 10 dake Legas zuwa ranar Lahadi. Kwamishinan INEC a jihar…

Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC ta ɗage zaɓen  gwamna da ɗan majalisar jiha a akwatuna 10 dake Legas zuwa ranar Lahadi.

Kwamishinan INEC a jihar Legas Olusegun Agbaje ne ya sanar da ɗage zaɓen da yammacin Asabar .

Ya ce ɗagewar ta shafi mazaɓu biyu dake Victoria Garden City a ƙaramar hukumar Eti-Osa.

Ya ƙara da cewa jami’an zaɓen da aka tura yankin ne suka ƙi gudanar da aikinsu saboda fargabar ƙalubalen da suka fuskanta a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.

“Don haka an ɗage gudanar da zaɓen sai gobe Lahadi da ƙarfe 8:30 na safe”.