Dan kwallon tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Fegor Ogude a ranar Talatar da ta wuce ne ya bayyana cewa sai da ya biya Naira miliyan 1 da dubu 300 kafin wadanda suka yi garkuwa da matarsa su sake ta.
A wata tattaunawa da ya yi da kafar watsa labarai ta The Cable, Ogude wanda yanzu haka yake buga kwallo a wani kulob mai suna Amkar Perm da ke Rasha ya ce sai da ya biya wadanda suka yi garkuwa da matarsa a Najeriya zunzurutun Naira miliyan 1 da dubu 300 maimakon Naira miliyan 30 da suka nemi ya biya sannan suka saki matarsa mai suna Maimunat.
Wannan bayani na dan kwallon ya ci karo da wanda jami’an tsaro na farin kaya (DSS) suka yi na cewa an saki matar dan kwallon ne ba tare da an biya ko sisin kwabo ba.
Idan za a tuna a ranar 4 ga watan nan ne aka samu labarin sace matar dan kwallon da wadansu suka yi a Warri na Jihar Delta. An ruwaito wadanda suka sace ta sun bukaci sai an biya su zunzurutun Naira miliyan 30 kafin su sake ta.
Sai dai bayan kwana 6 da sace ta ne sai Jami’in hulda da ’yan jarida na kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 (U-23) Mista Timi Ebikagboro ya bayar da sanarwar Maimunat ta samu ’yancinta, bayan an sake ta, amma bai yi wani karin bayani na ko an biya kudi ko a’a kafin a sake ta din ba.
Tun daga lokacin ne wasu ke ta rade-radin an biya makudan kudin kafin a sake ta. Daga baya Hukumar gudanar da bincike ta farin kaya (DSS) ta fitar da sanarwar cewa ba a biya ko sisin kwabo ba, amma kwatsam sai ga mijin Maimuna Fegr Ogude da ke wasa a Rasha ya nuna shi da kansa ya biya Naira miliyan 1 da dubu 300 kafin ta samu ’yancin kanta. Ya nuna bai yi nadamar yin haka ba, don matarsa ta fi muhimmanci a kan kudin da ya yi asara.
“Da yawa daga cikin wadanda ake garkuwa da su ba kasafai suke samun ’yanci ba tare da an hallaka su ba, don haka tilas na gode wa Allah da ya kubutar da Maimunat duk da kudin da na biya kafin a sake ta”, inji shi.
Garkuwa da mutane ba sabon abu ba ne a Najeriya musamman ma a Kudancin kasar nan.
Sai da na biya fiye da Naira miliyan 1 kafin a saki matata -dan kwallon Super Eagles Ugude
Dan kwallon tsakiya a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Fegor Ogude a ranar Talatar da ta wuce ne ya bayyana cewa sai da ya…