Al’ummar gundumar Dan-Aji dake karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina sun musanta ikirarin gwamnatin jihar Zamfara kan cewa ba a biya ko sisin kwabo ba kafin a sako ‘yan mata 26 da aka yi garkuwa da su a yankin.
Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya ce sun sami nasarar kubutar da ‘yan matan daga masu garkuwar ba tare da biyan kudin fansa ba.
- An ceto ‘yan mata 26 daga hannun masu garkuwa a Zamfara
- ’Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun yi garkuwa da mutum 17
Wasu majiyoyi sun shaidawa Aminiya cewa an sace ‘yan matan ne a kauyen Dan Aji dake kan iyaka da jihar Zamfara ranar 13 ga watan Oktoban 2020.
Majiyar ta kara da cewa, “Yawancin wadanda aka sace ‘yan mata ne, haka masu garkuwar suka rika bi gida-gida suna tsintarsu.”
“Ba su damu da daukar yara kanana ko tsofaffi ba, sai da suka zaba sannan suka tafi da matan, yawancinsu masu karancin shekaru da zawarawa,” inji wata majiyar.
Sai dai mai taimakawa gwamna Matawalle a kan harkokin watsa labarai da wayar da kan jama’a, Zailani Bappa ya ce an kubutar da matan ne bayan tattaunawa da maslaha da ‘yan bindigar.
Amma Dagacin garin Dan-Aji, Alhaji Lawal Dogara ya shaidawa ‘yan jarida ranar Litinin cewa sai da suka biya N6.6 kafin a sako yaran.
“Ya kamata gwamnan Zamfara ya daina neman suna da kubutar da ‘ya’yanmu, saboda sai da muka biya kudin fansa kafin a sake su,” inji shi.
Dagacin ya kuma ce sai da shugabannin al’umma biyu daga yankin, Alhaji Abdulkarim Dan Aji da Liman Babangida Dan-Aji suka yi tattaki na tsawon kwanaki uku a daji domin kai kudaden fansar kafin a saki yaran.