✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Safarar shanu a jirgin kasa: Fatake sun jinjina wa Buhari

Da misalin ƙarfe 3:30 na ranar Asabar ɗin da ta gabata ne jirgin farko ɗauke da shanu da raguna daga garin Gusau ya sauka a…

Da misalin ƙarfe 3:30 na ranar Asabar ɗin da ta gabata ne jirgin farko ɗauke da shanu da raguna daga garin Gusau ya sauka a kasuwar shanu ta Abbatuwa da Legas, wanda shi ne irinsa na farko a shekara 30 da suka shuɗe.
Muhammadu Altine Gusau, wakili ne na fataken shanun da ya biyo jirgin daga Gusau zuwa Legas, ya shaida wa Aminiya cewa dawowa da wannan tsari da Shugaba Buhari ya yi abin a jinjina masa ne. “Mun gode wa Allah da Ya nuna mana dawowar wannan harka. Rabonmu da ganin haka tun lokacin mulkin Buhari na soji, sai ga shi ya farfaɗo da shi a yanzu. Hakazalika ina jinjina wa Gwamnatin Zamfara da ƙungiyoyin fatake na jihar bisa jajircewarsu a harkar.”
Muhammad Altine Gusau wanda ya ce ya shafe sama da shekara 40 yana jigilar shanu a jirgin ƙasa, ya  ce ba su gamu da wani cikas ta a zo a gani ba a wannan tafiyar, sai dai tsaikon da suka ɗan samu kafin jirgin ya taso domin sai da lulumin asubahin Juma’a suka tashi da misalalin ƙarfe 4:00 na safe. Ya ce babban abin da gwamnati ya kamata ta mayar da hankali a kai shi ne, lafiyar jiragen da tsaron rai da dukiyoyin fataken, domin idan aka samu lalacewar jirgin hakan ka iya haifar da mumunar asara. Ya yi kira a shigo da taragan jirgi da suka yi daidai da na ɗaukar shanu. “kalubalen da muka fuskanta, ita ce jirgin ba na ɗaukar fasinja ba ne, da muka isa Kaduna ma’akatan jirgin sun yi yunƙurin ɗibar fasinja sai muka nuna ba mu yarda ba har rai ya so ya ɓaci. To bayan da na kira waya na yi ƙorafi ne aka sallame mu,” inji shi.
Alhaji Muhammad Bello dan kasuwa ne da jirgin ya sauke shanunsa, ya shaida wa Aminiya cewa sun yi matuƙar farin ciki amma fatarsu shi ne harkar ta ɗore, domin a yanzu an lasa musu zuma; ba su kuma fatan a wayi gari a ce babu jirgin.
Shgaban kungiyar Matasa Dilallan Shanu na Jihar Legas, Alhaji Muhammadu Tom, kira ya yi ga dilallan shanu su bai wa shirin na gwamnati goyon baya, domin fatake baƙi da suke kawo shanu su ci ribar wannan canji. “Jin daɗinsu shi ne namu, a gaskiya ne a rayuwa in an yi haƙuri canji zai zo, mu a yanzu canji ya zo mana domin fatake na ɗaukar mota a Naira dubu 150 zuwa 200 sai ga shi yanzu za su ba da Naira dubu 40 a kawo musu a jirgin ƙasa, a sauke kayan hankali kwance ba tare da wata matsala ba, ai babu wani abin farin ciki da ya wuce wannan,” inji shi.
Shi ma Kakakin kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyyeti Allah a Legas, Alhaji Salisu Jikan Toro, yaba wa gwamnati ya yi na dawo da sufurin shanu a jirgin ƙasa, domin a cewarsa wannan mataki ne na kawo sauƙi wanda Shugaba Buhari ya yi musu alƙawari. “Wannan harka ta sufuri za ta magance matsalar nan ta ɓarayin shanu wacce ta daɗe tana ci mana  tuwo a ƙwarya, domin shanun da jirgi zai kwaso sai an tantance ba kamar yadda ɓarayin shanu  za su kai mota daji su loda mata shanun sata ba, hanyar sufuri da jirgi hanya ce mafi tsabta in aka lura za a ga shanun da aka sauke suna cikin ƙoshin lafiya babu wata dabba da ta galabaita bare wadda aka yanka ai ka ga wannan ba ƙaramin ci gaba ba ne. Fatanmu su ƙara inganta aikin ba wai sauƙin kawai ba” inji shi.