✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sadiya Haruna ba ‘yar Kannywood ba ce —Alhassan Kwalli

"Wadda ake ta ke magana a kanta ba 'yar Kannywood ba ce."

Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finan Kannywood, Alhassan Kwalli ya ja hankalin jama’ar gari game da labaran da ake yada wa cewar Sadiya Haruna jaruma ce a Kannywood.

Jarumin, wanda yana daya daga cikin masu ruwa da tsaki a Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i (MOPPAN), ya ce Sadiya ba ta daga cikin jaruman masana’antar.

Alhassan Kwalli ya yi wannan fashin baki ne cikin wani hoton bidiyo na tsawo minti 2:50 da a yanzu ya yi shuhura a kafafen sada zumunta.

“Muna so mu ja hankalin Ummah Shehu da ta kiyaye harshenta da kuma lafazinta, sannan ta zauna lafiya kamar kowa.

“Sannan muna kara jan hankalinta cewar wadda ta ke magana a kanta ba ‘yar Kannywood ba ce, saboda na ga kafafen yada labarai sun dauka ‘yar Kannywood ce, ba ‘yar Kannywood ba ce.

“Saboda haka don Allah don Annabi, muna kira da abokan sana’armu da su san irin kawayen da za su dinga jawo mana cikin wannan masana’anta,” a cewarsa.

Daga karshe jarumin ya yi addu’ar samun rabauta daga ubangiji, da kuma addu’ar samun zaman lafiya a wasu yankuna na Najeriya da ake fama da matsalar tsaro.

Wannan martani na zuwa ne kan kama Sadiya Haruna da Hukumar Hisbah ta yi a ranar Juma’a tare da gurfanar da ita a gaban kotu da aka yanke mata hukuncin komawa makarantar Islamiyya na tsawon watanni shida.