✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sace mata 26: Tattaunawa kai tsaye da Bulama Bukarti

Babban abun kunya ne ga gwamnati da kuma Najeriya a matsayinta na kasa.

Barista Audu Bulama Bukarti gogaggen lauye ne mai fafutikar kare hakkin  kuma kwararren mai bincike a kan ta’addancin da ya addabi Najeriya musamman na Boko Haram a Arewa maso Gabashin kasar da kuma na ’yan bindiga a Arewa maso Yamma.

Aminiya ta tattauna da shi kan mata 26 da aka yi garkuwa da su a Jihar Katsina suka kuma kubuta bayan iyalansu sun biya kudin fansa.

Bulama Bakarti ya shaida wa wakiliyarmu cewa lamarin babban abun kunya ne ga gwamnati da Najeriya.

Kwararen lauyan ya yi tir tare da bayyana damuwa kan tabarbarewar matsalar tsaro musamman a Arewacin Najeriya.

Ya buga misali da yadda maharan suka dauke matan ciki har da kananan yara masu shekaru 10 suka shafe makonni suna musu fyade ba tare da gwamnati ta dauki mataki ba.

Bukarti ya ce abin damuwa ne yadda labarin dauke su bai yadu ba sai bayan wallafa rahoton binciken kwakwaf da jaridar Daily Trust ta yi a kai bayan kubutarsu.

Masanin ya ce matsalar tsaro da halin ko in kula daga bangaren gwamnati ya kai munzali na intaha.

Ta’addancin ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewacin Najeriya

Bulama ya ce ba a Najeriya kadai ta’addanci ya ke karuwa ba, domin kuwa a halin yanzu kungiyoyin ta’adda a fadin duniya na karuwa tare da samun karin karfi a turbar tasu.

Ya ce bisa al’ada ’yan ta’adda kan fara ne ba tare da wata kwarewa ba, amma bayan duk harin da suka kai suka cimma nasara sukan samu kudi ta hanyar karbar kudin fansa ko fashi; har daga baya su gawurta su mallaki muggan makamai da magoya baya daga daidaikun mutane.

Hakan ne ya ce ke faruwa a Najeriya, ’yan ta’adda na kara cin karensu babu babbaka saboda duk harin da suka kai suka samu nasara na sa su ji sun gawurta sun kuma kara gogewa.

Bukarti ya ce ’yan ta’adda musamman a Arewa maso Yammacin Najeriya na kara karfi tunda suka fara addabar yankin shekara 8 zuwa 10 da suka gabata.

Kasawar Gwamnati da hukumomin tsaro

Dalili na biyu da ya ce ya sanya ta’addanci karuwa a Arewa shi ne gazawar gwamnati da hukumomin tsaro, duba da yadda suka kasa sauke nauyin tsare rayuka da dukiyoyin al’umma da ya rataya a wuyansu.

Kwararren masanin shari’ar ya ce jami’an tsaro musamman ’yan sanda sun yi karanci a Najeriya.

Ba kuma a ba su horo ko kwarewar da ta kamace su ballantana a inganta walwala da jin dadin da suka cancanta a yi musu ba.

Bugu da kari galibinsu zalunci, cin hanci da rashawa su riga sun yi katutu a zukantansu.

Ba matsalar talauci ba ce

Bulama ya ce rashin wadatar da kasar da jami’an tsaro da kuma ba su nagartattun makamai don kiyaye doka da oda ba lamari ne na rashin arziki a Najeriya ba.

Ya ce irin rayuwar alfarma da ministoci da shugaban Kasa ke yi shaida ne cewa a kan cewa akwai tarin arziki a Najeriya amma ana fifita amfani da arzikin ne a bangarori marasa fa’ida.

“Rayuwar jin dadi da sanatoci, gwamnoni, kwamishinoni da ’ya’yansu ke yi na nuna irin rashin kishin kasa da yadda masu rike da madafun iko a kasar nan suka fifita jin dadin kansu fiye da kare martabar kasar.

“’Ya’yansu suna karatu a mafi tsadar makarantu a Turai, kuma motsi kadan su fice daga kasar jinyar cutar da ba ta taka kara ta karya ba kamar ciwon wuya ko ciwon kunne.

“Rashin damuwa da halin ko in kula da gwamnatin Najeriya ke yi ya jefa mu cikin mawuyacin halin da muke fuskanta kuma ko kadan kasar nan ba ta bukatar fita neman taimako daga kasashen duniya idan aka duba irin arzikin da take da shi.”