Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya yi wa fursunoni 11 afuwa albarkacin shiga sabuwar shekarar 2023.
Ya yi haka ne bisa sahalewar da Sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
- Ya kona makaranta bayan sace mata kwamfutoci a Binuwai
- Mun kama bako da kullin hodar iblis 105 daga Brazil —NDLEA
Fadar Gwamnatin Jihar ta ce, Gwmanan ya aikata hakan ne bisa shawarar da Majalisar Tausayawa ta jihar ta bayar kan yi wa fursunonin afuwa a ranar Sabuwar Shekara.
Sanarwar ta ce yi wa fursunoni afuwa al’ada ce wadda gwamnatin jihar ta saba a duk sabuwar shekara.
Cikin sakon sabuwar shekarar da ya aike, El-Rufai ya yi wa al’umar jihar fatan alheri tare da ba su tabbacin samun sauki duk da tsadar rayuwa da ake fuskanta.
Wadanda afuwar ta shafa sun hada da Musa John da Yakubu Abdullahi da Habu Usman da Shamsu Usman da Abdullahi Abdulmumuni.
Sauran su ne, Mahadi Abdullahi da Futune Mabuke da Abdullahi Lawal da Sunday Iliya da Mohammed Anas da kuma Kayode Gabriel Adenji.