✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabuwar kungiyar mawaka ta bayyana a Jihar Katsina

A makon jiya ne aka kaddamar da shugabannin da za su rike sabuwar kungiyar mawaka mai suna ‘Waka Babbar Hikima,’ mai taken ‘Gonar Da Ta…

A makon jiya ne aka kaddamar da shugabannin da za su rike sabuwar kungiyar mawaka mai suna ‘Waka Babbar Hikima,’ mai taken ‘Gonar Da Ta Wuce Ratse’ a dakin taro na Katsina Motel.

kungiyar wadda ta samo asali daga dandali a shafin nan na sada zumunta (Facebook), ta samu halarcin mawaka da dama wadanda kuma suke matasa ne.
Nufin kungiyar hada kan mawakan da suka hada da na gargajiya da kuma na zamani, domin ciyar da wannan sashe gaba. Kamar yadda shugaban taron wanda kuma yake Mataimakin Shugaban Kwalejin Ilmi ta Tarayya (FCE) Katsina, Dokta Aliyu Idris Maikaji ya ce, kafa irin wadannan kungiyoyi na da matukar tasiri idan aka lura da tasirin waka a tsakanin al’umma, ba wai ga Bahaushe ba kadai.
Doktan ya yi nuni da irin yadda ake samun wasu kalamai daga mawakan da za a ga ana amfani da su a wajen wasu maganganun na yau da kullum, inda ya ba da misali da cewa: “Ta hanyar waka ce aka samo maganar nan da ake cewa, ‘Yan amshin Shata.’ Bayan kuma kowa ya san cewa Shata mawaki ne.”
Sai dai shugaban taron kuma uba ga wannan sabuwar kungiya, ya ja hankalin membobin kungiyar da su hada kai da junansu, kada su bari Shedan ya shiga tsakaninsu.
Shi ma a nasa bangaren, uban taro kuma uba ga duk wasu kungiyoyi da ke fadin Jihar Katsina, Alhaji Amadu Nafuntuwa (Sa’in Katsina) ya ce: “In dai har za a yi wa Annabi waka, ashe waka ta zamo wani abu ce mai muhimmaci.” A kan haka ne ya hori ’ya’yan wannan kungiya da su rike wannan sana’a da kyau.
Haka kuma ya kawo masu misali da irinsu Alfazazi mawakin Ishiriniya, da Marigayi Abubakar Ladan da su Mamman Shata da sauransu a kan irin gudunmuwar da suka ba da ta wajen habaka harshe da al’ada da kuma kishin kasa da sauransu.
Tun farko sai da shugaban riko na wannan kungiya, Misbahu Ganuwa ya bayyana dalilansu na kafa wannan kungiya, wadanda suka hada da kokarin ciyar da harshen Hausa da al’adun Bahaushe gaba ta hanyar hikimar waka, wadda in aka lura hatta da wasu kabilun sun fi mayar da hankali a kan koyar da addinin Islama ta hanyar wakoki. Ya kawo misali da kabilar Yarabawa, wadanda suka yi amannar duk abin da aka koyar ta hanyar waka yana da wuya ya fita daga cikin zukatan wadanda aka koyar.
Har ila yau, shugaban ya roki manya da su shige masu a gaba, domin aza su bisa hanya a inda suka ga sun yi ba daidai ba.
An dai rera wakoki na nan take, a yayin wannan biki na kaddamar da wadannan shuwagabanni na riko, mai yawan membobin da suka kai 76, wadanda suka hada da Misbahu Ganuwa a matsayin shugaba, Usman Hamza, mataimaki, Malam Salisu Arabi, sakatare, Babangida Dogo, ma’aji tare da jami’in hulda da jama’a; Malam Musa Firishiyos da sauransu.