✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sabuwar kungiya ta kunno kai a APC ta Kano

Kungiyar tana tare da Jam’iyyar APC kuma tana aiki ne a karkashinta.

Wata sabuwar kungiya mai suna Patriotic Volunteers Association, ta bullo a cikin Jam’iyyar APC ta Kano da nufin bayar da gudunmawar samar da sahihan ’yan takara a badi.

Wani tsohon Kwamishinan a Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Dan Azumi Gwarzo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a madadin kungiyar a wani taro da suka gudanar a cibiyar ’yan jarida ta jihar.

Alhaji Dan Azumi Gwarzo ya ce, a yayin da babban zaben badi ke karatowa don ganin komai ya tafi yadda ake bukata, ya zama dole a bayar da shawarwari don ganin an cimma nasara.

Ya kara da cewa ya zama dole a bi ka’idojin dimokuradiyya don samar da tsarin shugabanci mai karfi da kuma inganci.

Ya ce, manufar kungiyar ita ce samar da ingantaccen tsarin shugabanci nagari da gudanar da mulki bisa ka’ida da ya dace da ka’idojin kasa da kasa.

A cewarsa, kungiyar tana tare da Jam’iyyar APC kuma tana aiki ne a karkashinta.