Barkanmu da sake haduwa da ku a wannan fili na girke-girke.
Da fatar uwargida tana gwada irin nau’o’in girke-girken da muke kawo muku.
Canja girki ga maigidana kara dankon so da kauna.
Kamar yadda na saba sanar da ku akwai hanyoyi da dama da za a bi wajen sarrafa kaza.
Don haka a yau na kawo muku sabuwar hanyar gasa kaza.
Abubuwan da za a bukata
- Kaza daya
- Magi
- Kori
- Attarugu
- Garin tafarnuwa
- Garin kwakwa (za a samu a manyan shaguna)
- Albasa
- Man gyada
Da farko uwargida za ta wanke kazarta yadda ba za ta yi karni ba.
Sannan ta yanka ta kanana ta ajiye a gefe.
Sai ta hura wuta har ta yi garwashi sai ta dora karfen gashi a kai.
Sannan ta samu kwano mai fadi ta jajjaga attarugu ta zuba.
Ta sa magi daidai dandano ta hada da kori da garin kwakwa da na tafarnuwa.
Sai ta kwaba su sosai sannan ta tsoma kazar a ciki.
Sannan sai ta kai cikin firij ta ajiye na tsawon minti 10 zuwa 15.
Bayan haka, sai ta yanka albasa babba guda daya ta dora a kan karfen gashi.
Sannan ta dora kazar a kai.
Haka za ta yi ta juyawa har sai ta gasu tare da yaryada mata man gyada.