Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usuman Alkali Baba ya karbi ragamar jagorancin Rundunar daga hannun Mohammed Adamu mai barin gado.
Alkali ya karbi aiki shugabancin ne a Hedikwatar Rundunar, jim kadan bayan Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya daura masa sabon mukaminsa a ranar Laraba a Fadar Shugban Kasa.
Bikin mika ragamar shugabancin Rundunar ga Alkali yana gudana ne a dakin taro na Rundunar, inda manyan hafsoshin suka hallara.
Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi ne ya sanar da nadinsa a ranar Talata, washegarin wasu kazaman hare-hare da aka kai a Hedikwatar ’Yan Sanda da gidan Yari a Jihar Imo, inda aka saki tsararru sama da 2,000.
Ra’ayoyin ’yan Najeriya kan nadin Alkali
Tuni dai ra’ayoyin ’yan Najeriya suka bambanta kan nadin da aka yi wa Alkali a matsayin Mukaddashin Sufeto Janar na ’Yan Sandan.
Wasu ’yan sanda da muka zanta da su sun bayyana cewa ba su da wata matsala da shi, amma duk da haka, kamata ya yi wanda aka nada ya kasance Mataimakin Sufeto Janar (DIG) ba Mukaddashin DIG ba.
“Dama Sabon Mukadashin Sufeto Janar din mu Mukaddashin DIG ne, na so a ce DIG ne aka nada ya maye gurbin tsohon Sufeto Janar.
“Ba ni da wata matsala da kowannensu kuma ban san wata doka da ta saba wa yin hakan da aka yi a yanzu ba, amma wasu abubuwan ba daidai ake yinsu ba,” inji wani jami’in dan sanda.
Wani dan sanda da muka zanta da shi kuma ya ce jami’an ’yan sanda na ta addu’ar Allah Ya sa sabon Sufeto Janar din ya magance hare-haren da ake kai wa ’yan sanda a baya-bayan nan.