Sarkin Zazzau na 19, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya shiga fadarsa da ke birnin Zariya a ranar Laraba.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal, na tare da Sarki Bamalli a lokacin da ya isa fadar tasa bayan sanar da nadin sa.
A ranar Laraba 7 ga Satumba, 2020 Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da nadin Sarki Ahmed Bamalli, wanda ta ce ya fara aiki nan take.
Nadin ya zo ne washegarin wata doguwar ganawa da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi da Majalisar Sarakunan Jihar.
- Ahmed Bamalli ya zama Sarkin Zazzau na 19
- Yadda ake zaben sabon Sarkin Zazzau
- Tarihi da rayuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris (1937-2020)
A ranar Talata gwamnan, yayin gabatar da kasafin kudin jihar na 2021 ya ce nan gaba zai mika wa Majalisar Dokokin Jihar kudurin dokar sauya tsarin masarautun jihar.
Kalaman nasa sun zo ne a lokacin da ake jiran tsammanin nadin Sarki na 19 a Masarautar Zazzau wadda ita ce mafi girma a Jihar Kaduna.
Tun ranar 20 ga Satumba, 2020 Allah Ya yi wa Sarki na 18, Alhaji Shehu Idris rasuwa, sai dai ba a nada magajinsa ba sai bayan kwana 17.
Rahotanni sun nuna cewa an yi ta kai ruwa rana tsakanin Gwamna El-Rufai da Masu Zabar Sarkin Masarautar game da sunayen da za a zabi sabon sarki daga ciki.
Majiyarmu ta ce gwamnan ya umarci masu zabar sarkin su yi watsi da sunayen ukun da suka fara mika masa daga cikin ‘yan takara 11 masu neman kujerar su sake sabon zabe amma masu zaben sarkin suka ce babu bukata domin sun yi zaben ne cikin adalci.
Kafin kalaman gwamnan a zauren majalisar, an yi ta rade-radin cewa zai raba Masarautar Zazzau zuwa gida uku, Zazzau, Kudan da kuma Kaduna.
Sai dai wasu makusanta a Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna sun ce dokar ba za ta shafi masarautar Zazzau ba, sauye-sauye kawai za ta yi ga wasu dokokin sarauta da turawan mulkin mallaka suka yi.
A wancan lokaci sunan Bamalli , ba ya cikin ‘yan takara uku da Masu Zabar Sarki suka tura wa Gwamna El-Rufai.
Masu sharhi na ganin kusancinsa da gwamnan ta taka rawa a neman neman a sake lalen sunaye da aka yi wanda Masu Zabar Sarkin suka ki amincewa su yi.