✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sabon samfurin COVID-19 mai suna ‘IHU’ ya bulla a Faransa

Samfurin dai na da nau'o'i 46, kuma ya kama mutum 12.

A daidai lokacin da duniya ke ci gaba da fama da barazanar samfurin COVID-19 na Omicron mai saurin yaduwa, masana ilimin kimiyya sun sake gano wani sabon samfurin mai suna ‘IHU’.

Binciken dai ya gano sabon samfurin na da nau’o’i har 46, kuma ya zuwa yanzu ya kama mutum 12 a kasar Faransa, kamar yadda jaridar Independent ta rawaito.

A cewar binciken, an gano mutum na farko da ya kamu da cutar ya yi tafiya a ’yan kwanakin nan zuwa kasar Kamaru, kamar yadda masu binciken suka wallafa a mujallar medRxiv.

To sai dai masana sun yi gargadin cewa ba lallai ne don an gano samfurin ya kasance yana da saurin yaduwa kamar ragowar samfuran ba, ciki kuwa har da na Omicron.

Sabon binciken dai ya gano cewa sabon samfurin na da nau’uka har 46, wadanda ba a kai gano su a wasu kasashen ba bayan Faransan, kuma ba ya cikin samfurin da binciken Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) gano a baya.

Bugu da kari, masu binciken sun yi ikirarin cewa mutumin da aka samu da samfurin na IHU an yi masa cikakkiyar rigakafin COVID-19.

“Mutum uku na baya da aka gwada kuma aka gano, sakamakonsu bai yi iri daya da na Delta ba, wanda yake ajin kwayoyi na SARS-CoV-2 a lokacin,” inji masu binciken.

A wani dogon sako da ya wallafa a shafin Twitter, wani masanin kwayoyin cututtuka a Kungiyar Masana Ilimin Kimiyya ta Amurka, Eric Feigl Ding, ya ce suna ci gaba da nazari a kan sabon samfurin domin gano saurin yaduwarsa da kuma girman barazanarsa.