A makon da ya gabata, farmaki da ‘yan bindiga ke kaiwa Jihar Katsina ya dauki sabon salo.
An samu masu shigar mata da abaya, a yayin da wasunsu ke yin shigar buzaye su nade jikinsu da makamai su afka wa mutanen gari.
Yawaitar hare-haren a jihar ya sa mutanen yakunan da abun ya shafa yin zanga-zangar lumana da neman Shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus.
A wani hari da suka kai, ‘yan bindigar sanye da abaya da suka yi shigar mata, sun je Sabuwar Unguwa a garin Kurfi, inda suka sace mutane biyu tare da harbin mutum daya.
Mutanen gari na ganin hakan na iya zama barazana ga mata a garuruwan da abun ke faruwa, musamman saboda shiga ce ta addinin Musulunci.
Har wa yau a cikin watan, an kai hari na biyu, inda ‘yan bindigar suka bad da sawu da kayan mata, suka sace wata yarinya.
Said dai shugaban ‘yan banga yankin, Nura Liman, ya ce sun gano lagon farmakin da ‘yan bindigar suke kai musu kuma za su dau mataki.
“Daga yanzu, mun yi dokar mata ba za su rika fita yawo ba in har karfe 8:00 ya wuce”, inji shi.
– Sun saci jiki sun shiga garin
Wata majiya ta ce, a lokacin farmakin da ‘yan bindigar suka kai, wanda ‘yan bangar suka dau mataki a kai, maharan su 20 suka ijiye mashinansu a wani tsauni da ke bayan gari.
Ya ce sun kuma shiga cikin garin sanye da kayan mata da misalin karfe 9:00 na dare.
Mutanen gari sun ce maharan sun boye bindigoginsu ne a cikin rigunansu, kuma duhun dare ya taimaka musu wajen yin ta’addanci. A lokacin ne ‘yan bindigar suka sace wasu mata biyu a garin.
Suka ce, a farmakin Lahadin da gabata ne suka kama ‘yar Shugaban Kula da Harkokin Daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsin-ma, Dakta Muttaka Mamman.
– Yadda maharan suka yi ta’asa
Majiyar ta ce an dauke yarinyar ne tare da wata mata mai ‘yaya bakwai, Murja Umar, sai kuma mijin matar Ibrahim ‘Yar Gashe da suka harba da bindiga. Yana asibiti amma da sauki.
A jawabin baban yariyar, ya ce an kai farmakin ne da misalin karfe 9:00 na dare.
“Yarinyar suna dawowa ne da yayanta Umar daga gidan goggonsu aka sace ta. Yaron ya ce yaga mutanen su 10 sanye sa hijabi sun tukaro su sai bai yarda da su ba. Ta yi kokarin guduwa amma daya daga cikinsu ya bi ta kofar gidan ya kama ta”.
Ya ce kuma har yanzu mutanen ba su tuntube shi ba.
Shamsiya Faruk, wadda ta kubuta daga hannun ‘yan bigidigar ta ce “Na ji harbin bindiga lokacin da muka fara cin abinci da mijina. Na yi yunkuri rugawa waje amma mai gidana ya rike ni.
“‘Yar uwata Murja na ji tana rokon a taimake ta da karfi. Na turkari kofa na bude, sai daya daga cikinsu ya rike mini kafa. Allah Ya taimake ni na fizge kafata na gudu”, inji ta
Ta ce, a lokacin da take kokarin kubuta, mijinta na janta, shi kuma dan bindigar na ja. “Dan bindigar ya harbi mijina amma bai same shi ba”.
A nashi jawabi, mijin nata, Faruk Mohammed, cewa ya yi, “Matata na bude kofar aka yi harbi da ya sami kofa. Kingin kiris da ya same ni. Kaga ramin da ya yi wa kofar can. Allah Ya sa ba ni da karar kwana.
“Da karfi suka tafi da Murja duk da ihun da ta yi ta yi na a taimake ta”.
Mijin wata wadda aka sace, Ahmed Kurfi, wanda tsohon direba ne ya ce sace matarsa da aka yi ya sa shi cikin rudani.
– Sun shammaci mutanen gari
“Ina masallaci na ji harbin bindiga, da isowa gida na tarar abun ya faru”.
Wasu mutanen gari da suka ga yadda lamarin ya faru sun ce an yi musu bazata.
Daya daga cikinsu, Mohammed Lawal ya ce, “Muna zaune cikin duhu sai muka ji harbin bindiga, kafin ka ankara kowa ya watse”.
Sai dai kuma a wasu garuruwan, abun ya faskara, mutanen duk sun yi hijira son su tsira da ransu.
– Mutane sun yi gudun hijira
Shamsiyya ita ce wadda Allah Ya taimaka ta tsira makonni biyu da suka gabata, lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki garuruwan Kureci da Giye da Gurza da Gurzan Kuka da Makanwaci da Didu da Ukalawa da Tsasr Mangwaro da Sanawa da kuma Unguwar Bera dake Karamar Hukumar Dutsin-ma.
Ta ce maharan sun sace dabbobi da dama, kuma kauyawan da dama sun gudu sun bar garuruwan.
Da Aminiya ta ziyarci garuruwan a ranar Asabar, an ga yara da mata suna hijira dauke da sauran kayayyakinsu
Fatima Abbas, wadda ta yi gudun hijira daga kauyen Dogon Ruwa ta ce “Na ji tsoron kar a kashe ni ne, dole in yi hijira daga garin saboda harin da aka kai mana”.
– Jami’a ta hana ma’aikatanta zuwa aiki
Saboda tsoron harin, Jami’ar Gwamnatin Tarayya Ta Dutsin-ma da ke kusa da garuruwan ta hana ma’aikatanta zuwa aiki wurin.
A takardar da mai magana da yawun makarantar, Habibu Matazu ya fitar, Shugaban Makarantar, Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi, ya umarci ma’aikata su rika aiki daga tsohuwa jam’iar na zuwa wani lokacin.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isa, ya tabbatar da cewa ‘yan bindigar dauke da bingigogi kirar AK47 sun kai farmakin kauyen suna harbe-harbe.
– Jami’an tsaro na kokarin magance matsalar
Ya ce sun yi garkuwa da wata yarinya kuma suka harbi wani mutum Ibrahim Yar Gashe a kafa, amma yana samun sauki a asibitin da aka kai shi.
“Mayakan soji na Operation Puff Adder da Saran Daji suna kokarin kwato yarinyar”, inji Isa.
Ya ce, ‘yan sanda na bakin kokarinsu na ganin sun kawo karshen ‘yan bindigar a Katsina. Ya ce sun kashe ‘yan bindiga uku makonni uku da suka wuce, sun kuma kwato babur uki da shanu 30 da tumaki 60.
“Mun kuma kama mutum uku da ake zargin ‘yan bindiga ne”.