✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sabon rikici ya barke tsakanin Sadiya Haruna da Fati Slow

Sadiya ta ce an kai mata hari a shagonta, inda ta yi zargin ana so ne a watsa mata acid a fuskarta.

A wani sabon rikici a tsakanin jaruman mata, an samu wani faifan bidiyo na Sadiya Haruna tana kuka, inda take cewa lallai tana neman agajin mutane domin rayuwarta na cikin hadari.

A cikin bidiyon, ta ce an kai mata hari a shagonta, inda ta yi zargin ana so ne a watsa mata ruwan guba na acid a fuskarta.

Ta kuma yi zargin an kama kaninta da zargin satar waya, inda ta ce kaninta ya fi karfin ya saci waya.

A cikin bidiyon, ta yi zargi wasu da ce mara tsoron Allah da mace da na namiji.

Jim kadan kuma sai ga bidiyon Fati Slow, inda ta je kai tsaye ta kira sunan Sadiya Haruna ta ce ba hari aka kai mata ba, ’yan sanda ne suka je kama ta, amma ta gudu.

A cewar Fati Slow, Teema Makamashi ta wuce da sanin Sadiya Haruna. Ana cikin hakan ne, sai Chizo Germany ya fitar da wani bidiyon, inda yake yin kira da a sanya baki a rikicin na Sadiya Haruna da Teema Makamshi.

A cewarsa, ya sha ya shirya tsakaninsu, amma kuma daga baya su ci gaba. A karshe ya yi kira ga mahukunta a Kannyood da masu fada a ji a Jihar Kano da sanya baki domin a samu maslaha.

Ya kara da cewa ya san duk abubuwan da suka kawo rigimar, amma shi ba zai dauki bangare ba, domin duk mutanensa ne, amma ya musu kashedin cewa idan ya fara bude magana fa akwai matsala