Rahotanni sun bayyana cewar mutane kusan dubu 14 ke kokarin tserewa daga yankin Kudancin Sudan ta Kudu domin gujewa barkewar wani sabon tashin hankali.
Mutanen na ficewa ne sakamakon yadda aka kwashe kwanaki biyar ana gwabza fada tsakanin dakarun mataimakin shugaban kasar Riek Machar da na magabatansa da suka bi bayan sahun shugaba Salva Kiir a garin Leer da ke a Kudancin kasar inda nan ne mahaifar Riek Mashar.
- Matawalle ya yi martani kan raba wa Sarakunan Zamfara motoci na alfarma
- Tarayyar Turai za ta fara sayen gas daga Najeriya don rage dogaro da Rasha
Wani ganau ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP cewar sojojojin sun kai hari a kauyukansu inda suka kona gidaje tare da kwashe shanu da awaki.
A cikin wata sanarwa da ya bayyana, wakilin Majilisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu ya ce an wawashe kauyuka da dama da ke kudu da garin Leer da kuma lalata tashar jiragen ruwa ta Adok da ke a kan gokin Nilu, sai dai bai bayyana wanda ke da alhakin yin haka ba.