Sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Idrisu Dauda Dabban, ya lashi takobin ganin bayan ’yan bindiga da ma sauran mutanen da suka addabi Jihar.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya shiga ofis don fara aiki ranar Juma’a a Katsina, inda ya roki hadin kai da goyon bayan sauran jami’ansa don ganin burin nasa ya cika.
- Dailin direbobin motocin daukar mai na fasa yajin aiki
- Rasha za ta yi gwajin makaman Nukiliya ana tsaka da zaman dardar tsakaninta da Ukraine
Sai dai ya ce hakarsa ba za ta kai ga cimma ruwa ba matukar bai samu cikakken hadin kai daga jami’ansa a Jihar ba.
Ya ce, “Masu aikata laifi mun san abin da za mu yi musu. Za mu kama su mu kai su gaban shari’a. Tsohon Kwamishinan ya yi kokari, kuma Insha Allahu za mu dora daga inda ya tsaya.
“Ba mu da wani magani, Allah shi ne mai magani, amma Insha Allahu za mu san abin da za mu yi,” inji Kwamishinan.
CP Idrisu ya kuma roki jama’ar Jihar da su taimaka wa jami’ansa da bayanan da za su kai ga fallasa ayyukan bata-gari a Jihar.
A ranar Larabar da ta gabate ne dai Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya nada shi mukamin bayan daga likafar tsohon Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Buba Sanusi, wanda yanzu ya zama Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sandan.
Kafin nadin nasa dai, CP Idrisu shi ne Kwamishina mai kula da harkokin sadarwa a hedkwatar rundunar ta kasa da ke Abuja.