✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sabon hari ya ci rayuka a Kudancin Kaduna

Akalla mutum 14 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai kauyen Mado da ke karkashin masarautar Atyap ta Karamar Hukumar Zangon…

Akalla mutum 14 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai kauyen Mado da ke karkashin masarautar Atyap ta Karamar Hukumar Zangon Kataf a wani hari da aka kai ranar asabar da daddare.

Harin, wanda wasu ‘yan bindiga da ba a kai ga tantance ko su waye ba suka kai da misalin karfe 11:30 zuwa 12:00, ya jikkata wasu mutum uku tare da kona gidaje guda uku.

A wani harin mai kama da na daukar fansa, wasu maharan sun kewaye wata rugar Fulani da ke kauyen Kankada kan hanyar Madakiya zuwa Zonkwa da ke Masarautar Bajju a Karamar Hukumar ta Zangon Kataf da safiyar Lahadi inda suka kona rugar kurmus.

Wata da ta tsallake rijiya da baya, Halima Haruna, ta shaida wa Aminiya cewa ba su san hawa ba ba su san sauka ba suka wayi gari an kewaye su tare da kona musu gidaje ana farautar mutanensu.

“Daga baya ne mu ka ji wai sun zo daukar fansar harin da aka kai ne a wani kauye wanda ba abinda mu ka hada da su,” in ji ta.

Halima, wacce matar Ardon rugar ne na Kankada, ta shaida wa Aminiya cewa sun shiga mummunan hali da takaici kasancewar zaman lafiyar da su ke yi a wurin da ko kazar wani ba su taba kashewa ba amma aka kawo musu hari.

“Sai da mu ka kwashe awa uku a boye kafin jami’an tsaro suka kawo mana dauki.

“A yanzu haka muna ofishin ’yan sanda na garin Zonkwa kuma bamu san irin barnar da su ka yi mana ba yanzu ni dai da ido na na ga gawar mutanenmu guda biyu namiji da mace.

“Yayin da maharan suka bazama cikin daji neman Fulaninmu da suka gudu cikin daji don tsira da rayukansu don haka bamu san halin da suke ciki ba a halin yanzu,” a cewar ta.

Da yake magana da Aminiya ta wayar tarho, Shugaban Kwamitin Samar da Tsaro da Zaman Lafiya na Masarautar Atyap, Mista John Bala Gora, ya yi tir da da lamarin.

Ya ce abin takaici ne da kullum hare-hare ke ta kara ci gaba a yankin Karamar Hukumar duk da irin tashi tsayen da ake yi don wayar da kan jama’a kan illar kashe-kashe.

Da yake tabbatar wa da Aminiya dukkanin hare-haren guda biyu, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige ya ce tuni tawagarsu ta tseratar da mutanen kauyen na Kankada a karkashin jagorancin shugaban ’yan sanda na yankin Kafanchan.

ASP Jalige, a madadin Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kaduna, Abdullahi Mudassiru, ya kirayi mutanen Karamar Hukumar Zangon Kataf da na Kudancin Kaduna gaba daya, da su guji daukar doka a hannunsu kuma su guji hare-haren ramuwar gayya.