Sabon Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya, Manjo-Janar Farouk Yahaya ya riki ludayin kama aiki ranar Juma’a 28 ga watan Mayun 2021.
Janar Yahaya ya kama aiki ne a matsayin wanda ya rike mukamin karo na 11 a tarihi tun bayan dawowar kasar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999.
A ranar Alhamis da ta gabata ce Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasar bayan rasuwar Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru da ke rike da mukamin.
Ana iya tuna cewa, a ranar Juma’ar makon jiya ce, Janar Attahiru da wasu manya da kananan hafsoshin soji suka riga mu gidan gaskiya samakon wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da su a Jihar Kaduna.
Sai akwai yiwuwar manyan jami’an sojin Najeriya masu mukamin Janar har kimanin 30 za su yi murabus na dole, biyo bayan nadin da aka yi wa Manjo-Janar Yahaya a matsayin Babban Hafsan Sojin Kasar.
Aminiya ta yi wannan hasashe ne yayin da bisa al’ada a hukumomin tsaro na kaki, idan aka nada sabon shugaba a cikinsu, wajibi ne dukkan jami’an da ke gabansa da mukami su yi murabus.
Babu shakka Manjo-Janar Yahaya yana cikin manyan jami’an soji ’yan ajin kwas na 37, wanda shi karami ne idan aka kalli jami’an da suka shiga aikin soji ’yan ajin kwas na 35 da na 36.