Gwamnatin Filato ta amince ta fara biya ma’aikatan Kananan Hukumomi a fadin jihar da sabon mafin karancin albashi na N30,000.
Hakan na zuwa ne bayan zanga-zangar da ma’aikatan kananan hukumomin jihar 17 suka gundanar na tsawon lokaci a garin Jos, suna neman a biya su da sabon albashin na N30,000.
- Lambar NIN: Ba za a rufe layukan waya ba
- An ceoto mutum 77 daga masu garkuwa a Katsina
- Miji ya tsere bayan Matarsa ta haifi ’Yan hudu
- Masu Umrah sun rasu a hanyar zuwa Makkah
Daga karshe dai a ranar Alhamis Gwamnatin Jihar ta amince fara biyan ma’aikatan kananan hukumomin, kamar yadda suka bukata.
Wata sanarwa da ke dauke da sanya hanun Babban Sakataren Hukumar Kananan Hukumomin Jihar, Henry K. Lankwap ce ta bayyana haka.
Sanarwar ta ci gaba da cewa Gwamnatin Jihar Filato, ta amince da hakan ne a taron gaggawa da ta yi a Gidan Gwamnatin Jihar.
Ya ce gwamnatin ta umarci Hukumar Ma’aikatan Kananan Hukumomin ta shirya dukkan wasu tsare-tsare na ganin an fara biyan ma’aikatan da sabon albashin batare da bata lokaci ba.