Rahotanni na nuna cewa sabbin takardun kudin da gwamnati ta sahale fara amfani da su daga ranar Alhamis sun kare tas a bankunan Najeriya.
Bayanai dai na nuna cewa a jihohi irinsu Legas da Abuja da Kano, tun karfe 12;00 na ranar Alhamis din suka ce sun kare.
- Abin da ya sa Tinubu da Atiku kasa ambaton jam’iyyunsu
- Hafsoshi 122 sun samu karin girma zuwa matsayin Janar
Wani ma’aikacin Bankin Access reshen Ojodu da ke jihar Legas da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce N100,000 na takaradar N1,000 kacal aka raba wa masu bada kudi ta kanta a bankin, don raba wa kwastamomin da suka zo cirar kudi.
“Baya ga haka ma ba mu da sabbin takardun N500 da N200. A takaice dai, kudi kadan aka ba mu mu dinga bai wa mutane.
A hannu guda kuma wasu bankunan sun koka kan yadda al’umma ke gudun sabbin kudin idan sun zo karbar kudi.
Shi ma wani ma’aikacin bankin ya ce a wasu jihohin ma da dama daga kudu da Arewa, suna samun rahoton wasu daga cikin kwastomomin ba sa karba saboda a cewarsu, mutane ba za su karba ba a kasuwa.
“Mutane kalilan ne a nan yau suka amince da sabbin kudi a kanta idan mun ba su, saboda da yawan ’yan kasuwa gudunsu suke yi saboda wai kwastamominsu za su bar su da su,” inji ma’aikacin.
Baya ga bankuna kuma, na’urorin cirar kudi (ATM) da dama tsofaffin takardun suke bayarwa kamar yadda al’umma da dama suka bayyana.
“Ni dai har tambaya nake a wacce na’urar cirar kudi zan samu sababbn kudi amma shiru ban gamu da wanda ya samu ba.
“Na je banki aka bani na da,” inji wani dan kasuwa a Kano.
Ita ma wata ma’aikaciya cewa ta yi, “har sakawa na yi a turo min kudi don na samu cire sabbi amma sam ba labari”.
“Watakila sai an kwana biyu za su shigo mana.
Rahotanni sun ce bankuna da dama sun dinga bai wa kwastamominsu hakuri, saboda a cewarsu har yanzu suma sabbin ba su shigo hannunsu ba tukunna.