✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN Ya Kori Ma’aikata 117 A Cikin Kwanaki 20

Muna cike da fargaba saboda ba mu san wadanda korar za ta biyo ta kansu ba.

Babban Bankin Najeriya CBN ya ƙara korar wasu ma’aikatansa 50 a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Wannan kakkaba da ake yi a bankin karkashin shugabancin Mista Olayemi Cardoso ya shafi bangarori 29 na bankin.

Kididdigar da muka yi Gwamnan Bankin Cardoso ya kori ma’aikata 117 daga ranar 15 ga Maris ɗin da ya gabata zuwa Litinin, 8 ga Afrilu, 2024.

Korar ta shafi daraktoci da mataimakan daraktoci, manyan manajoji, da kuma ƙananan ma’aikata daga ɓangarori daban-daban na bankin.

Kawo yanzu babu wani ƙwaƙƙwaran dalili da Cardoso ya bayyana a matsayin abin da ya sa yake wannan bugun ’ya’yan kadanya a bankin.

Wani da ke da masaniyar halin da ma’aikata a bankin ke ciki ya ce, hankalin dukkan ma’aikatan babban bankin na tashe, saboda babu wanda ya san waɗanne abubuwa ake dubawa a sallami mutum daga aiki.”

Duk iya kokarin da manema labarai ke yi na sanin dalilin wannan aiki ya ci tura, domin jami’an babba bankin sun yi gum kan dalilin matakin.

Ko a jiya Laraba 10 ga Afrilu 2024 mun tuntuɓi jami’ar dake da alhakin hulɗa da manema labarai, Hakama Sidi Ali amma ba mu same ta ba.

A kwanakin baya dai Aminiya ta ruwaito cewa ana korar duk wani da ya yi aiki daf da tsohon gwamnan bankin da a halin yanzu yake shingen Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, Godwin Emefiele.

Sai dai har kawo yanzu, hukumar bankin ba ta musa zargin ba, kuma ba ta fito ta bayyana wani abu daban a matsayin dalilin ba.

Wata majiya mai tushe da ta buƙaci a sakaya sunanta wadda kuma ba ta da izinin yin magana a kan lamarin, ta shaida wa wakilinmu cewa za a ci gaba da korar ma’aikata har zuwa ƙarshen watan Afrilu.

Ma’aikatan da lamarin ya shafa, da suka zanta da Aminiya bisa sharaɗin sakaya sunansu, sun ce rashin fayyace hujjar korarsu ta sa suna ganin cewa Mista Cardoso na yin ramuwar gayya ne kawai.

Abin Da Yasa Ma’aikatan Ke Damuwa

Babban abin da ke ci wa ma’aikatan da abin ya shafa tuwo a kwarya shi ne zargin “nuna bambanci da mahukuntan na yanzu su ke yi.” wurin korar.

Wasiƙun sallamar da aka aike wa daraktocin da wasu ma’aikatan da abin ya shafa, kamar yadda wakilinmu ya gani, na ɗauke da saƙon, “Sake fasalin tsarin mulki da na ma’aikata” a matsayin dalilin korar su.

Mun gano cewa akwai daraktoci biyar da ke shirin maka bankin a kotu bisa zargin korarsu ba bisa ka’ida ko wani dalili ba.

Sun ce, “an kore mu ba bisa ka’ida ba, babu wani laifi da aka kama mu da shi, kuma babu wani mai laifi da ya ambaci sunanmu a gaban kotu”.

Akwai ’Ya’an Bowa Da Na Mowa A CBN

Wani babba a bankin na CBN ya bayyana wa Aminiya cewa akwai shafaffu da mai a CBN.

Ya ce, akwai wanda ana ganin za a koresu a sashin da suke, an canza musu sashen aiki sun koma karkashin gwamnan kai tsaye.

Akwai wadanda aka mayar da su Legas amma sun bi waɗansu hanyoyi an dawo da su kusa da Abuja.

Tanadin Kundin Tsarin Aiki A CBN

Sashi na sha shida, sakin layi na uku, lamba na biyar a cikin baka; ya bayyana cewa, ya kamata ma’aikaci ya yi ritayar kammala aiki a ranar da ma’aikaci ya cika shekara 60 da haihuwa, ko kuma ya kai shekaru 35 yana aiki.

Sannan kundin tsarin aikin ya bai wa hukumar gudanarwa ta babban bankin kasar damar sallamar ma’aikacin da ya kai shekara goma yana aiki da su.

Kundin tsarin ya bayyana lokacin barin aiki a matsayin lokacin murnar ba da gudunmawa ga bankin.

Sai dai kuma sashi na sha shida sakin layi na huɗu ya bayyana cewa akwai sallamar aiki da ke samuwa sanadiyyar yawan ma’aikata.

An tsara wannan ne domin ba da dama ga hukumar bankin ta kawo sauye sauye masu ma’ana.

Kundin ya bayyana cewa daga cikin dalilan da za a  buƙaci a dakatar da ma’aikaci akwai matsalar tattalin arziki, samun sabuwar fasahar zamani, kawo sabon tsari ko kuma wasu dalilai makamanta haka.

Muna Rayuwa Cikin Fargaba — Ma’aikata

Da yawa daga cikin ma’aikatan babban bankin da suka zanta da wakilinmu sun ce suna rayuwa cikin fargaba saboda ba su da tabbacin wanda korar za ta biyo ta kansa.

Daya daga cikin ma’aikatan ya ce: “Mun ga ana korar ba gaira ba dalili a bangaren saye da sayarwa na bankin.

“Kazalika an yi kora ta gayya a bangaren kuɗaɗen raya kasa da kuma sashin kula da lafiya.

“Ina cike da fargabar cewa za a kori duk waɗanda suka yi aiki daf da daraktocin da aka kora. Aiki da fargaba yana iya zama kalubale ga ingancin aiki.”

Wani babban ma’aikacin ya ce: “Mutane da yawa da aka kora a sulale suka bar ofisoshinsu cikin kaduwa da firgici.

“Hakika babu wanda ya isa ya taimaki waɗanda ake kora, abin a tsare yake.”

Abin Na Shafar Abokan Hulɗar CBN

Wakilinmu ya gano cewa, abokan hulɗar CBN da su ka yi kwantiragi suka gama na cikin wani hali.

Domin kuwa kuɗaɗensu da suka bari wurin gudanar da waɗansu ayyuka na neman makalewa bisa zargin cewa sun ci gajiyar aiki da gwamnatin tsohon gwamna Godwin Emefiele.

Wata majiya mai tushe ta shaida mana cewa, wadanda ke da uwa a gindin murhu cikin ‘yan kwangilar sun samawa kansu mafita, domin kawo yanzu sun bi hanyoyi kuma ana aiki a kan takardunsu domin biyansu hakkinsu.