Sabbin manyan hafsoshin soji sun isa birnin Maiduguri na Jihar Borno domin ganawa da masu ruwa da tsaki da zummar tumke damarar ci gaba ba da tunkarar ta’addancin masu tayar kayar baya.
Hafsan Hafsoshin Soji, Manjo Janar Leo Irabor ne ya jagoranci tawagar manyan sojin zuwa hedikwatar Rundunar Operation Lafiya Dole ta Sojin Sama da ke Maiduguri da misalin karfe 1.30 na ranar Lahadi.
- NDLEA ta kama mace da hodar Iblis ta N30bn
- COVID-19: An sanar da ranar sake bude makarantu a jihar Filato
Aminiya ta samu cewa wani jirgin sama ne ya yi jigilar manyan hafsoshin sojin zuwa Maiduguri da suka hada da Hafsan Hafsoshin Soji; Manjo Janar Leo Irabor da Hafsan Sojin Kasa; Manjo Janar Ibrahim Attahiru da Hafsan Sojin Ruwa; Rear Admiral Awwal Gambo da kuma Hafsan Sojin Sama; Air Vice Marshal Isiaka Amao.
Wata majiya ta ce ziyarar da manyan hafsoshin sojin suka kai Maiduguri na da nasaba ne da shimfida sabbin dabarun samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin na Arewa maso Gabas.
A makon jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami tsoffin manyan hafsoshin sojin Najeriya inda ya maye girbinsu bayan an dade ana kiraye-kiraye a kan hakan.