✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabbin kudi: Makiyaya sun roki Buhari ya kori Gwamnan CBN

Kungiyar ta kuma roki a dage wa'adin daina karbar tsohon kudi har zuwa watan Disamban 2023

Kungiyar makiyaya ta Kulen Allah a Najeriya (KACRAN) ta yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya kori Gwamnan Babban Bankin kasar, Godwin Emefiele.

Kungiyar ta kuma roki Shugaban da ya kara wa’adin da babban bankin ya bayar na daina amfani da tsohon kudin har zuwa watan Disamban 2023.

A cikin wata sanarwa da Shugabanta, Khalid Muhammad Bello, ya sanya wa hannu kuma ta fitar ranar Talata a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, kungiyar ta ce, ya zama wajibi a yi wannan kiran bisa wasu dalilai.

A cewar sanarwar, “Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya jefa ’yan Najeriya cikin kunci da tsarinmu na hada-hadar kudi a cikin da rudani da gangan, saboda sake canza launin wasu tsofaffin takardun kudaden da aka yi da kuma bullo da sabbin takardun kudi na Naira.

“Gazawar Babban Bankin CBN na samar da isassun takardun kudi na naira don zagayawa ya zama abin damuwa ga KACRAN, domin wannan ya haifar da wahalhalu maras amfani ga ’yan Najeriya da dama musamman mazauna karkara da makiyayanmu.

“Yayin da ya rage ’yan kwanaki kadan a yi watsi da tsofaffin kudaden, da yawa daga cikin mambobinmu da suka yi watsi da dabbobinsu don neman canza tsohon kudinsu, tuni suka shiga cikin damuwa da asarar kudi da ba za a iya misaltawa ba.”

Haka kuma, saboda karancin kudin da ke yawo a fadin kasar nan har da Abuja, karfin sayayyar al’umma  ya ragu matuka, don haka ana samun cikas wajen biyan kudin magani, abinci da sauran hada-hadar kudade na gaggawa, lamarin da ya haifar da wahalhalu ga  mutane.

“Abin kunya ne a ce Gwamnan CBN, shi kadai ya kitsa tare da aiwatar da wannan shiri mai cike da cece-ku-ce da rashin jin dadi hatta ga Ministar Kudi.

“Har ila yau, abin takaici ne yadda Gwamnan na CBN, ya yi gaggawar aiwatar da wannan shirin ba tare da samar da isassun kudaden da za a ba bankunanmu da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi ba, ciki har da cibiyoyin POS da ake ba abokan huldar su a madadinsu.

“Ya manta da cewa, Nijeriya na tafiyar da tsarin mulkin dimokuradiyya wanda dole ne a ji ra’ayin mutane ko kuma a yi amfani da su kafin aiwatar da manufofin gwamnati.

“Da gangan ya ki sauraron duk kiraye-kirayen kishin da ’yan Najeriya suka yi na a kara wa’adin karbar tsohon kudin.

“Matsayin da ya dauka na dakatar da tattara tsofaffin takardun kafin ranar 31 ga watan Janairu, 2023, ya firgita ‘yan Najeriya sosai tare da aika mummunan sako ga talakawan makiyayanmu da ’yan kasuwa da ke zaune a cikin kurmi ko kuma a lungu da sako na kasar,” in ji sanarwar.

Daga nan sai kungiyar ta roki Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da shirin daina amfani da tsohon kudin nan da 31 ga watan na Maris, har zuwa karshe watan Disamba don kauce wa jefa ’yan kasa cikin halin kaka-ni-ka-yi.