Za a bude sabbin jami’o’i na tarayya da kuma kwalejin ilimi na tarayya da zummar bunkasa ilimi mai zurfi a Najeriya.
Majalisar Datttawa ta amcince a kafa Jamiar Harkokin Jiragen Ruwa ta Najeriya a Okerenkoko a Jihar Delta da kuma Jami’ar Fasaha ta Tarayya a Auchi, Jihar Edo.
Za kuma a kafa Kwalejin Ilimi na Tarayya a Karamar Hukumar Giwa da ke Jihar Kaduna.
Zaman Majalisar na ranar Laraba ya kammala karatu a kan kudurin kafa manyan makarantun bayan karbar rahoton Kwamitin Majalisar kan Manyan Makarantu da Asusun Tallafa wa Ilimi Mai Zurfi (TETFUND).
Sanata Uba Sani daga jihar Kaduna ya gabatar da kudurin kafa kwalejin ilimi a Giwa yayin da Sanata James Manager daga jihar Delta ya gabatar da na jam’iar jiragen ruwa.
Shi kuma Sanata Francis Alimikhena daga jihar Edo ya gabatar da kudurin kafa jami’ar fasaha ta Auchi.