✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sababbin Gwamnoni sun fara alkawura:

Ni na kowa ne – Bindow  Zababben Gwamnan Jihar Adamawa Sanata Sanata Umaru Jibrilla Bindow ya ce shi na kowa ne. Kuma ba zai nuna…

Ni na kowa ne – Bindow 

Zababben Gwamnan Jihar Adamawa Sanata Sanata Umaru Jibrilla Bindow ya ce shi na kowa ne. Kuma ba zai nuna bambancin addini ko kabila jam’iyya a lokacin shugabancinsa ba.
Sanata Bindow ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi jim kadan da bayyana nasararsa a ofishin Jam’iyyar APC da ke Yola fadar jihar.
“Ina mai matukar nuna godiyata ga jama’ar Jihar Adamawa musamman wadanda suka goya mana baya kuma wadanda sanadiyyar kuri’unsu ne na samu nasara. Ina so na tabbatar wa jama’ar Adamawa cewa ni Gwamnan kowa ne kuma ba zan nuna bambancin jam’’iyya ko kabila ko addini ba,” inji shi.
Sanata Umaru Bindow ya sake mika godiyarsa ga wasu jam’iyyu kuma ya yi musu alkawarin kawo ci gaba a jihar. “Mu hada kai domin mu samu ci gaban jiharmu. Ina sake nuna godiyata kan gudunmawar zababben Shugaban kasa Janar Buhari da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar kan gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarata,” inji shi.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana nasarar Bindow a matsayin abin tarihi kuma ta kawo karshen masu siyasar kabilanci. “Yau ta zame mana rana mai kunshe da tarihi a jiharmu. Domin a yau wanda ake adawa da shi ya yi nasara kuma abu ne da ba a taba yi ba a jihar,” inji shi.
Ya kara da cewa “Bindow ya samu nasara ne sakamakon goyon baya da ya samu ga jama’ar Najeriya da suke neman canji. Kuma mun yi alkawari za a samu canji mai ma’ana da yardar Allah nan ba da jimawa ba.”
Atiku ya bukaci zababben Gwamna Sanata Bindow ya rike amana tare da cika alkawuran da ya dauka wa mutanen jihar. Ya bayyana bangarorin da suke neman gyara a jihar kamar harkar noma da kiwon lafiya da makarantu da yadda za a taimaka wa ’yan gudun hijira su koma gidajensu da samar da tsaro mai inganci.

Ba zan yarda da almubazzaranci da dukiyar jama’a ba – Bagudu

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

Zababben Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci almubazzaranci da dukiyar jama’a ko kauce ka’ida ba.
Zababben Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai, jim kadan da bayyana nasararsa a zaben Gwamnan Jihar da aka gudanar ranar Asabar.
Sanata Abubakar Bagudu ya yi alkawarin yin gaskiya wajen tafiyar da dukiyar Jihar Kebbi, inda ya sha alwashin sanya kafar wando daya da duk wani jami’i da zai yi yunkurin danne hakkin jama’a, “Ba zan danne hakkin jama’a ba, kuma ba zan kyale wani ya danne hakkinsu ba,” inji shi.
Ya mika ta’aziyya da jaje ga iyalan wadanda suka rasu ko suka samu rauni a lokacin da aka gudanar da zaben da ya gabata, inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnati mai zuwa ba za ta ba al’ummar jihar kunya ba.
Sanata Bagudu ya ce, matsalolin da suke addabar jihar ba za a magance su ba, sai tare da goyon bayan al’ummar jihar gaba daya, don haka ya ce akwai bukatar jama’ar jihar su ba da gudunmawar da ta dace domin ci gaban jihar da kasa baki daya.
Ya gode wa al’ummar jihar a kan zaben da suka yi masa don kasancewa gwamnan Jihar Kebbi.

Lalong ya yi alkawarin biyan ma’aikatan Filato albashin da suke bi

Daga Husaini Isah, Jos

Zababben Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya yi alkawarin biyan dukkan albashin da ma’aikatan jihar suke bi bashi.
Barista Simon Lalong ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos, bayan an bayyana cewa shi ne ya lashe zaben Gwamnan jihar.
Ya ce, “Za mu fara ne da tunkarar babbar matsalar nan ta rashin biyan albashin ma’aikata a jihar nan, wadda ta kawo rashin jin dadi ga al’umma. Dole ne mu biya ma’aikata albashin da suke bi,
ko bashi ne za mu ciwo, domin mu biya ma’aikata albashin da suke bi,” inji shi.
Zababben Gwamnan ya ce za su tafi da dukkan kabilun da suke zaune a jihar domin a samu zaman lafiya da ci gaba.
A daren ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta bayyana cewa Barista Simon Lalong na Jam’iyyar APC ne ya lashen zaben Gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar da kuri’a dubu 564 da 913, inda ya kayar da babban abokin karawarsa Sanata Gyang Pwajok na Jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’au dubu 520 da 627, kamar yadda babban jami’in tattara sakamakon zaben Farfesa Emmanuel Kucha, ya bayyana wa manema labarai, inda ya ce
Barista Simon Lalong ya samu kuri’a mafiya jinjaye kuma ya cika dukkan ka’idojin da ake bukata.

Babu cuwa-cuwa a gwamnatina – Barista Abubakar

Daga Hamza Aliyu, Bauchi

Zababben Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar APC, Barista Mohammed Abdullahi Abubakar ya ce gwamnatinsa za ta toshe dukkan hanyoyin da ake facaka da kudin al’umma a gwamnatance inda ya ce bai kamata Gwamna ya rika wasa da kudin talakawa ba.
Zababben Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyi kai-tsaye a Gidan Talabijin din Jihar (BATb) a ranar Litinin da maraice.
Ya ce ya kamata al’umma su fahimci cewa gwamnatinsa ba za ta rika daukar makudan kudi tana raba wa wasu mutane ’yan tsirari ba, don haka zai fi bada fifiko wajen samar wa matasa hanyoyin samun kudin shiga.
M.D. Abubakar ya kara da cewa akwai kauyuka da dama da ya ziyarta a lokacin kamfen da suke bukatar kayan inganta rayuwa kuma ya yi musu alkawarin da zarar ya kama aiki zai ba da fifiko wajen bunkasa rayuwar mutanen karkara.
Ya ce ina tabbatar wa al’umma cewa babu cuwa-cuwa a gwamnatina don haka duk wanda muka samu yana wasa da kudin al’umma zai dandana kudarsa.

Za mu ba da ilimi kyauta daga firamare zuwa jami’a – Gwamna Gaidam

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Zababben Gwamnan Jihar Yobe, kuma Gwamna mai ci Alhaji Ibrahim Gaidam, ya yi albishir ga al’ummar jihar cewa, zai ba da ilimi kyauta daga firamare har zuwa jami’a idan kudin shigar jihar ya inganta da nufin al’ummar jihar su kara morar romon dimokuradiyya.
Gwamna Gaidam ya bada wannan tabbaci ne ya yin da yake ganawa da manyan ’yan siyasar jihar da suka kai masa ziyarar taya murnar lashe zabe a gidan gwamnati da ke Damaturu.
Gwamna Gaidam ya ce, kasancewar ilimi shi ne gishirin zaman duniya akwai bukatar gwamnatinsa ta kara yunkuri don ganin ta kai harkokin ilimi gaci musamman yadda aka bar jihar a baya a harkokin ilimi da tabarbarewar tsaro da karancin kudin shiga a jihar da tarayya suka taimaka kan faruwar haka.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta gina wani katafaren fillin jirgin sama na kasa da kasa, domin yin haka zai kara habaka tattalin arzikin jihar da al’ummarta sakamakon bunkasar harkokin kasuwanci da za a samu.
Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce ya yi imanin cewa sabuwar gwamnatin APC da za ta kama mulki za ta kawo karshen halin karancin kudi da kasar nan ke ciki ta yadda al’umma za su dara.