A kalla mutum 35 ne kotun tafi-da-gidanka ta hukunta a Jihar Edo a ranar Alhamis bayan da ta kama su da laifukan saba dokokin hanya.
Ajiye mota a kan hanya ba bisa ka’ida ba, sauke bafasinja a wuraren da aka haramta, rashin kiyaye ka’idojin tuki da sauransu, na daga cikin laifukan da aka aikata da kotun ta ce ba ta yarda da hakan ba.
Lauyan gwamnatin jihar, Mista Ayo Aigbokhiade, ya ce a kwaryar birnin Benin aka kama duka masu lafin.
Alkalin kotun, Mutairu Oare, ya ba da umarnin duka masu laifin kowannensu ya biya tarar N25,000 a cikin kwana biyu.
Sai dai alkalin ya ci daya daga cikinsu tarar N40,000 saboda daukar fasinja da ya yi a dandalin King’s Square.
An sallami wasu mutum biyu daga cikin wadanda aka gurfanar wa kotun saboda ba a same su da aikata kowane laifi ba.