Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja ta fara aiwatar da dokar hana amfani da lambobin motar ’yan sanda na musamman na (SPY).
Jami’ar Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Josephine Adeh ce ta bayyana hakan cikin sanarwar da ta fitar ranar Alhamis a Abuja.
A ranar Larabar ne dai Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba, ya haramta bayarwa da kuma amfani da wadannan lambobin na SPY a fadin kasa.
Baba ya ce an dauki haramta amfani da lambobin ne domin hana yadda wasu masu amfani da lambar ba su martaba dokokin hanya.
Domin tabbatar da bin dokar, shugaban ’yan sandan, ya umarci rundunar ta baza jami’anta kan hanyoyin Abuja a ranar Alhamis domin kwace lambobin a duk abin hawan da aka gani da ita.
Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Babaji Sunday, ya ce haramta amfani da lambar na da nasaba da yadda jama’a ke yawan korafi cewa masu amfani da lambar suna saba dokokin hanya tare da tozarta damar da suka samu.
Ya ce hakan zai taimaka wajen karfafa tsare-tsaren na yaki da manyan laifuka a kwaryar birnin Abuja.
Don haka Kwamishinan ya yi kira ga mazauna da su rungumi sabuwar dokar kana su bai wa ’yan sanda hadin kan da ya dace don su samu damar sauke nauyin da ya rataya a kansu.