Gwamnatin Jihar Neja, karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Sani Bello, ta kaddamar da Hukumar Kula da Kiyaye Dokokin Hanya ta Jiha (NISTMA).
Sanarwar da Sakatariyar Yada Labarai ga Gwamnan, Mary Noel-Berje ta fitar a ranar Talata, ta nuna cewa gwamnatin ta kuma kaddamar da motoci guda 21 wadanda hukumar za ta yi amfani da su wajen gudanar da ayyukanta a fadin jihar.
- Direban mota ya yi ajalin dan bunburutu da ‘ya‘yansa 2 a Abuja
- Al-Zawahiri: Wane ne shugaban Alka’idan da Amurka ta kashe?
Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar wanda ya gudana a harabar Babban Zauren Taro na Idris Legbo Kutigi da ke Minna, Gwamnan ya ce ya samar da sabuwar hukumar ce duba da Jihar Neja na da duka hanyoyin sufuri da ake amfani da su.
Ya ce NISTMA za ta taimaka wajen sanya ido kan kiyaye dokokin hanya da takaita matsalar tsaron da jihar ke fama da ita da kuma bunkasa kudin shigar jihar ta hanyar amfani da fasahar zamani.
“Hakkin sabuwar hukumar shi ne tabbatar da bin dokokin hanya don zirga-zirgar jama’a da kayayyaki cikin lumana, rage aukuwar hadurra da sauransu,” a cewar Gwamnan.
Kazalika, Bello ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su yi amfani da motocin da aka ba su yadda ya kamata, sannan su yi aiki tukuru wajen sauke nauyin da aka dora musu don cimma manufar kafar hukumar.
Ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin biyan albashin ma’aikatan hukumar na wata uku ne kacal, sannan bayan haka za a ci gaba da biyan albashin nasu daga kudin shigar da ma’aikatar za ta rika tarawa.
Sa’ilin da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron, Kwamishinan Sufuri na Jihar Neja, Barista Zakari Mohammed Tanko, ya ce a watan Yulin da ya gabata Gwamna Abubakar Sani Bello ya sanya wa dokar kafa hukumar hannu.