Sakamakon faduwar damunar bana, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta yi gargadin cewa akwai yuwuwar Najeriya ta fuskanci yawan hadurran jiragen sama a bana.
Hukumar ta kuma ce gargadin na da nasaba da yawan saukar ruwan saman da ake samu a bana wanda ta ce zai iya yi wa wuraren da jiragen kan yi tsere kafin su tashi a filayen sauka da tashinsu.
Darakta Janar na hukumar, Mustapha Habib Ahmed ne ya yi gargadin a Abuja yayin da yake gabatar da makala a kan magance aukuwar annoba a yayin wani taro kan harsashen yanayi na shekara-shekara na bana.
A cewarsa, “Za a fuskanci tsawa da kwanciyar ruwa da tsattsagewa da kuma malalar ruwa a wuraren tseren jirgin wadanda za su iya jawo tsaiko a tashi da saukar jiragen ko ma su haddasa soke zirga-zirgar wasu, kuma za su ma iya haddasa hatsari a wasu wuraren.”
Ya kuma ce akwai yuwuwar samun ambaliyar ruwa da zata iya lalata hanyoyi da gadoji ta kawo tarnaki a harkokin sufuri saboda ruwan da ake harsashen samu a bana ya fi na shekarun da suka gabata.
Sai dai ya ce ana harsashen samun karancin ruwa a Jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara da kuma Kano, yayin da Jihohin Legas da Osun kuma ake harsashen faduwar damunar ta bana a makare.
Shugaban na NEMA ya kuma ce akwai yuwuwar a sami ruwan sama fiya da yadda aka saba samu wanda kuma zai iya haddasa ambaliyar ruwa a Jihohin Borno da Yobe da Bauchi da Oyo da Enugu da Anambra da kuma Akwa Ibom.
Ya kuma ce kimanin Kananan Hukumomi 121 ne daga Jihohi 27 da Baban Birnin Tarayya Abuja ne ake harsashen za su iya fuskantar mummunar ambaliya, yayin da wasu 302 kuma za su fuskanci matsakaiciyar ambaliyar.