✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta yi wa mutum 500,000 barna a Habasha

Fiye da mutum dubu 500 ne ambaliyar ruwa ta shafa a Habasha, yayin da wasu yankunan kasar suka ce an samu ruwan saman da ba…

Fiye da mutum dubu 500 ne ambaliyar ruwa ta shafa a Habasha, yayin da wasu yankunan kasar suka ce an samu ruwan saman da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekara 100, kamar yadda Ministan Ruwa, Seleshi Bekele ya bayyana.

Ministan ya ce ambaliyar ruwan ta raba kimanin mutum dubu 200 da muhallansu a larduna biyar daga cikin lardunan kasar guda goma.

Ambaliyar ta kuma hallaka dabbobi tare da barnata amfanin gona da lalata gidaje da rusa ababen more rayuwar al’umma, wadda ba a taba ganin kwatankwacinta ba.

Yayin da lamarin ke kara muni a ’yan kwanakin nan, gwamnatin kasar ta fara rarraba kayayyakin agaji a wuraren da ambaliyar ta shafa ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu.

Kasar Sudan mai makwabtaka da Habasha ma ta fuskanci mummunan ambaliyar ruwa a bana.

Ambaliyar ta faru ne sakamakon sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka gani a daminar bana, inda yawan ruwan Kogin Nilu ya yi torokon da bai taba yi ba a cikin karnin nan.