’Yan Najeriya a kafafen sadarwa na zamani sun soki likin kudi da baki suka yi a wurin bikin diyar Shugaban Kasa, Hanan Muhammadu Buhari.
Da yawa sun rika kwatanta hakan da shirme da ya faru a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
An daura auren Hanan da mijinta Turad Sha’aban a Fadar Shugaban Kasa ranar Jumu’ar da ta gabata.
A bidiyon bukin, wadda Sahara Reporters suka wallafa a kafafen sadarwa na zamani an yi masa lakabi da “An yi ruwan kudi a bukin Hanan Buhari”, kuma ya jawo tsokaci daga akalla mutun 3,000 a Twitter da Facebook.
A cikin Bidiyon, an hasko Amarya Hanan da Agonta Turad suna taka rawa mutane kuma na musu liki.
Sai duk ta cewar bukin na ’yar shugaban kasa ne, ance ’yan sanda sun yi caraf da masu siyar da sabbin kudin da aka rika yin likin da su, amma daga baya an sake su.
Babban Bankin Kasa (CBN) ya kafa doka cewa duk wanda aka kama yana lika kudi, za a daure shi na wata shidda a gidan yari ko kuma tarar N50,000, kamar yadda Sashen na 21 na dokar CBN ta 2007 ta tanadar.