Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata kayan amfanin gona a kauyuka shida da ke cikin karamar hukumar Gumel a jihar Jigawa.
Kamfanin Dillanci Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa ruwan saman ya lalata fiye da gonaki 200 da kayan amfanin gona na kimanin Naira miliyan 500.
Jami’in Yada Labarai na Karamar Hukumar, Malam Sulaiman Usman, ya fada wa kamfanin dillacin labarai na Najeriya cewa kayan amfanin gonar da suka salwanta sun hada wake da masara da gero da kankana.
Ya ce garuruwan da bala’in ya aukawa sun hada da Garin Gambo da Gwari da Garin Galadima da Bilkarwa da Zuge da kuma Garin Baki.
Ya bayyana cewa manoman da suka amfana daga tallafin gwamnatin jihar a yankunan su ma bala’in ya shafe su.
Ya kara da cewa manoman da lamarin ya shaf sun nemi agajin gaggawa daga karamar hukumar da kuma gwamnatin jihar don kawo karshen matsalar.